Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ogbaru ta Jihar Anambra, Afam Ogene ya naɗa mataimaka 70 a mazaɓarsa.
Mista Afam Ogene ya ce, wannan mataki ya zo ne domin cika alƙawarin da ya dauka na samar da kyakkyawan aiki ga al’ummar mazaɓarsa.
- Abin da ya sa muka ƙara farashin man fetur — Tinubu
- Gobara ta yi ajalin ɗalibai 17 a makarantar firamare a Kenya
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da masu ba da shawara, mataimaka na musamman, mataimakan zartarwa da sauransu.
Takardar naɗin, ɗauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Ogene, Chinedum Uwolloh, wanda majiyar jaridar Punch ta gani a ranar Talata, ta bayyana irin nauyin da ke wuyan mataimakan.
Takardar ta bayyana cewa mataimakan za su “Taimaka wa ofishin Honorabul Ogene wajen cim ma babban burinsa na isar da kyakkyawan aiki ga al’ummar Mazaɓar Tarayya ta Ogbaru a yankin ko gudanar da duk wani aiki da ofishin ya ba su lokaci zuwa lokaci.
“An yi naɗin ne bisa gogewa da jajircewar waɗanda aka naɗa ga ɗan majalisar a matsayin wakilin mazaɓar da kuma jin daɗin Ogbaru.
“Ana sa ran sababbin mataimakan da aka nayda za su nuna ƙwarewarsu da kuma sha’awarsu ga muhimman ayyukansu, musamman wajen isar da ayyuka ga mazaɓar.
“Za su riƙa karɓar alawus-alawus na wata-wata da nufin ƙarfafa musu gwiwa da inganta yanayin tattalin arzikinsu.
“Wannan tallafin na kuɗi zai ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
“An yi nufin biyansu alawus-alawus ɗin ne domin a ƙara musu kuɗaɗen shiga, don ba su damar biyan buƙatunsu na yau da kullum da kuma mai da hankali kan samar da ayyuka na musamman ga Mazaɓar Tarayya ta Ogbaru,” in ji sanarwar.
Takardar ta kuma tunatar da cewa Ogene ya hau karagar mulki tare da yin alƙawari ga al’ummar mazaɓarsa da kuma Nijeriya, inda ya bayyana ƙudirinsa na yin shugabanci nagari.
“Alƙawarin da ya yi a bainar jama’a a watan Fabrairun 2024 yayin wani biki na godiya don murnar nasarar da ya samu a kotu, ya ce: ‘Na yi alƙawarin zama wakili mai hankali, mai riƙon amana, mai aiki tuƙuru don samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin mazaɓar Ogbaru.
“Zan ba da fifiko ga muradun jama’a, tabbatar da daidaito da adalci ga dukkan ’yan Nijeriya a cikin ayyukana na aiwatar da doka da sa-ido, bisa ƙa’idojin jagoranci.
“Na himmatu wajen inganta kishin ƙasa da gaskiya da riƙon amana a cikin ma’aikatun gwamnati, tare da samar da kyakkyawan tsarin gudanar da mulki. Don haka ina roƙon Allah Ya taimake ni!”
Daga cikin wadanda aka naɗa akwai: Mista David Chukwuekezie, Mai ba da Shawara ta Musamman (Siyasa); Ben Nwasike, Mashawarci na Musamman (Siyasa); Emmanuel Akpati, Shugaban Hulda da Jama’a; Maxwell Nwebo, Mataimaki na Musamman (Shirya tarurruka); Frank Oduah, Mataimakin na Musamman (Harkokin Ilimi); Tina Nwafor, Mataimakiya ta Musamman (Harkokin Mata); Amechi Ede, Babban Mataimaki (Al’amuran Addini) da sauransu.