Abdulwahab Umar Namadi ɗan farko ga Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya rasu, ya rasu ne bayan wani haɗarin mota kwana guda da rasuwar kakarsa a asibiti.
Abdulwahab mai shekara 24 wanda yake shi kaɗai a cikin mutanen da haɗarin ya rutsa da su ya rasu, yayin da abokinsa ya garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
Hajiya Maryam Namadi mahaifiyar gwamnan Jihar Jigawa ta rasu ne a ranar Laraba 25 ga watan Disamba, bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) kuma an yi jana’izarta a ranar.
An binne ta ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a garinsu na Kafin Hausa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Gwamnan ya tafi ƙasar China ne domin ziyarar aiki inda ya dawo jiharsa kai tsaye da safiyar Alhamis ranar 27 ga watan Disamba, 2024.