✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓata-gari sun lakaɗa wa masu adawa da Ganduje duka a Abuja

Muna so a mayar da jagorancin jam’iyyar APC yankin Arewa ta Tsakiya.

A ranar Alhamis ɗin nan ne wasu ɓata-gari suka lakaɗa wa masu zanga-zanga duka bayan dirar mikiya da suka yi a harabar Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki, inda suka buƙaci shugabanta na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus.

Masu zanga-zangar waɗanda suka fito daga otal ɗin Valential da ke Wuse 2, sun garzaya zuwa sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke kan titin Blantyre, inda wasu ɓata-gari ɗauke da sanduna suka far musu.

Ɓata-garin sun kuma ƙwace tutoci da kwalaye na masu zanga-zangar tare da lakaɗa wa wasu daga cikinsu duka.

Masu zanga-zangar da suka yi gudun tsira da rayukansu daga baya sun taru a wani fili a Wuse 2, inda shugabansu, Hamisu Suleiman Sardauna, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su tsige Ganduje tare da tabbatar da cewa an dawo da shugabanci yankin Arewa ta Tsakiya bisa kamar yadda tsarin rabon shiyya-shiyya na 2022 ya tanadar.

Sardauna ya ce, “Mu masu son zaman lafiya ne. Mu ‘yan wannan jam’iyya ne don haka babu wanda zai iya hana mu neman a yi adalci.

“Muna nan muna zanga-zangar lumana, amma wasu ’yan daba sun zagaya suna dukan mambobinmu. Wannan abin kunya ne.

“Muna fafutukar ganin an yi adalci. Dole masu ruwa da tsakin APC su mayar da jagorancin ofishin shugaban jam’iyyar na kasa zuwa yankin Arewa ta Tsakiya.

“Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da gwamnonin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen ganin sun yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.”