Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta yi hasashen cewar ƙananan hukumomin Jihar Zamfara takwas, za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana.
Babbar Darkatar hukumar, Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a birnin Gusau, yayin wani gangamin wayar da kai kan dabarun rage karfin ambaliyar ruwa ta hanyar yin gargadi da daukar matakai da wuri.
- An gudanar da sallah kan matsin rayuwa da tsaro a Jigawa
- NAFDAC ta gurfanar da masu sayar da jabun magunguna a Kano
Ta zayyano sunayen ƙananan hukumomin da ake hasashen ambaliyar za ta shafa da suka haɗa da; Bungudu, Gumi, Gusau, Bakura, Maradun, Talatar Mafar, Shinkafi da Zurmi.
Ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi aiki tare domin kare yankunan da ke cikin hatsarin ambaliya da muhimman kayayyakin more rayuwa tare da tallafa wa dorewar hada-hadar tattalin arziƙi a faɗin Najeriya, daga illolin ambaliyar ruwan.
Hasashen Hukumar Kula da Gudanawar Ruwa ta Najeriya (NIHSA), na bana ya nuna cewar jihohi 31 da ƙananan hukumomi 148 na cikin wuraren da ke cikin matsanancin hatsarin ambaliyar ruwa, yayin da jihohi 35, ciki har da Abuja, suka faɗa cikin wurare masu matsakaicin hatsarin ambaliya.
Hasashen ragowar ƙananan hukumomi 337 su kasance cikin wurare masu ƙaramin hatsarin ambaliya.
Ambaliyar ruwa dai na ci gaba da zama babbar barazana a wasu yankuna na Najeriya, inda kusan ko wace shekara ake samu asarar rayuka tare da dukiyoyi a sanadin ambaliyar.