✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan Majalisar jiha ya rasu a Kano

Ɗan majalisar ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Ɗan Majalisa mai wakiltar Kananan Hukumomin Bagwai da Shanono a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Halilu Kundila, ya rasu.

Kakakin majalisar, Ismail Falgore, ya jajanta wa iyalan marigayin a madadun daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar.

A cewar Falgore, Kundila ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa ya fitar, kakakin ya ce rasuwar ta girgiza majalisar da ma daukacin al’ummar jihar.

Ya kara da cewa rashin marigayin ba iya Kananan Hukumomin Shanono da Bagwai kadai zai shafa ba, har ma da al’ummar Kano baki daya.

“A wannan rana muna bakin cikin rashin ɗan uwanmu ɗan majalisar jiha, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Halilu Kundila, ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Shanono/Bagwai.

Falgore ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan Kundila, ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma bai wa iyalansa hakurin rashinsa.

Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.