✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓata suna: Tanimu Akawu ya nemi afuwar iyalan Ƙarƙuzu

Zan koma wannan filin tattaunawa na Gabon don gyara kuskurena. Nagode.

Sanannen ɗan wasan fim ɗin nan Tanimu Akawu ya nemi afuwar tsohon ɗan wasan Masana’antar Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Ƙarƙuzu, bisa kalaman da ya yi a kansa da iyalansa a wata hira da ta gudana kwanan nan.

Idan za a iya tunawa, a tattaunawar da aka yi da Akawu a cikin filin tattaunawa na ‘Gabon’s Talk show’, ya yi wani furuci, inda yake bayyana rashin jin daɗinsa a kan yadda ’ya’yan Ƙarƙuzu suke shakulatun ɓangaro da lafiyarsa duk da cewa mahaifin nasu (Ƙarƙuzu) yana fama da rashin lafiya.

Tanimu Akawu ya iƙirarin cewa, yana daga cikin waɗanda aka zaɓa su bai wa Ƙarƙuzu kayan abinci gami da kuɗi Naira dubu 400, saboda ’ya’yansa sun kasa kula da shi duk da halin da yake ciki na fama da jinya.

Wannan magana ta janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta wanda hakan ya wajabta wa Ƙarƙuzu fitowa don musanta abin da Akawu ya faɗi.

Ƙarƙuzu wanda a yanzu yake fama da makanta ya bayyana cewa, bai karɓi komai daga hannun Tanimu Akawu ba kamar yadda ya yi iƙirari, sannan batun rashin kulawa daga ’ya’yansa wannan ba gaskiya ba ce.

A gefe guda kuma, ɗaya daga cikin ’ya’yan dattijon, shi ma ya fito ya musanta abin da Akawu ya faɗi tare da barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan jarumin saboda ya so ya ɓata wa zuriyarsu suna.

Haka kuma a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sada zumunta an ga Tanimu Akawu ya fito yana neman afuwar iyalan Ƙarƙuzu, inda ya ce ya san ya yi kuskure. Kuma bai yi cikakken bincike ba kafin sakin zancen.

“Ina so in yi amfani da wannan damar in nemi afuwar Baba Ƙarƙuzu da iyalansa, a kan maganganun da na yi a hirar ‘Gabon’s Talk Show’ bisa rashin sani. Ina fatan shi da iyalansa za su yafe min.

“Sannan ina roƙon ɗaukacin masoyana su taimaka min wurin neman afuwar iyalan nan. Zan koma wannan filin tattaunawa na Gabon don gyara kuskurena. Nagode,” in ji Tanimu Akawu.

Ba wannan ne karo na farko da Tanimu Akawu ke tayar da ƙura a Masana’antar Kannywood ba.

Misali a watan Agustan shekarar 2019 ya musanta zargin da aka ce ya yi a kafafen sadarwar zamani cewa ya zargi mata ’yan fim da bin maza domin samun kuɗi, inda aka ce a cikin zargin ya ambaci sunan Hadiza Gabon da Maryam Yahaya yana misali da wayoyin hannun Maryam da kuma motar Gabon cewa ko shi da ya daɗe a harkar fim ba zai iya saya ba.

Sai dai Akawu ya musanta wannan zargi, inda ya ce ƙazafi da sharri da ƙarya aka yi masa, kamar yadda ya shaida wa Aminiya.

Ya ce, tabbas ya yi hirar da ake magana da gidan rediyon Human Right Radio, amma bai ambaci sunan kowace ’yar fim ba, balle ya kira ta karuwa.

“A gaskiya ba ni ba ne, na yi baƙin ciki da wannan labari, a zahirin gaskiya kimanin wata bakwai da suka wuce na yi hira da gidan rediyon Human Rights da ke Abuja, an naɗi muryata, an kuma ɗauke ni a bidiyo, babu wurin da na kira sunan Hadiza Gabon ko Maryam Yahaya sannan na kira su da sunan karuwai.

“Hadiza Gabon ta kira abokin aikina Al-Amin Buhari kasancewar ba ta da lambata, ni ma ba ni da tata, Al’Amin ya sanar da ita ba abin da na faɗa ba ke nan.

“Na samu labarin ma ta yi iƙirarin kai ni ƙara, amma ta je gidan rediyon Human Rights ɗin ta gane ba abin da na faɗa ba ke nan.

“An tambaye ni ko me ya sa mata ’yan fim suka fi maza kuɗi da famtamawa, sai na ce dole su fi mu, domin suna yin kwalliya, kuma suna da samari masu kuɗi da za su ba su kuɗi, mu kuma maza ba a ba mu.

“Amma ban ambaci sunan kowa ba. An tambaye ni ko ta yaya suke samun kuɗi, na ce wa mai tambayar ya je ya tambaye su,” in ji shi.