Sadeeƙ Umar da ake yi wa laƙabi da Mane, matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne da yake tashen taka leda a rukunin ’yan dagaji a Jihar Kano.
Matashin, wanda tauraronsa ke haskawa a fagen tamola ya yi fice ne bayan da ya kafa wani sabon tarihi na zura ƙwallaye 10 a raga a wasanni 10 da ya buga tare da ba da taimako sau 6 wajen wasu ƙwallayen a rukuni gasar wasannin ’yan dagaji aji 1 da aka fi sani da Amateur 1 a Jihar Kano.
- An ciro gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari
- Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
A cikin tattaunawarsa da Aminiya, Sadeeƙ Mane ya bayyana cewa, ƙwazo da sadaukar da kai ne suka taimaka masa wajen kafa wanna tarihi.
Sadeeƙ, wanda kamar sauran ‘yan wasa ya fara buga ƙwallon ne a cikin unguwa kafin daga bisani ya fara buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Togo da ke Unguwar Birget, Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
Daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Togo, Sadeeƙ ya koma taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Legend FC, inda a can ne bayan ya nuna bajinta a Gasar Cin Kofin Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta SBS Waliyya da ke buga wasa a matakin Amauteur 1 ta ɗauke shi.
A kakar bana Saƙeeƙ ya kafa tarihi, inda ya buga wasanni goma kuma ya zura ƙwallaye goma a raga.
Wannan nasara da ya samu ta sa ya lashe kyautar ɗan wasan da ya fi kowanne ɗan wasa zura ƙallaye a raga a wannan shekara.
Haka kuma an zaɓi Saƙeed a matsayin ɗan wasan da ya fi kowanne ɗan wasa ƙwarewa a wannan matakin.
Da yake ƙarin bayani kan yadda ya samu nasarar zura ƙwallaye 10 a cikin wasanni 10, Sadeeƙ ya ce, “na buga wasanni 10 kuma na zura ƙwallaye 10 a ragar abokan karawa.
A cikin wasanni 10 ɗin na zura ƙwallayen ne a wasanni 8, wato wasa 2 kacal ne ban ci ƙwallo ba. Wannan ne ya sa na zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a gasar.”
Da yake amsa tambayar ko me ne sirrin wannan nasarori haka?
Sadeeƙ Umar sai ya ce: “Ka san an ce in ka ji wane ba banza ba, wato in ba a sha gumi ba a sha rana. Don haka na jajirce ne da ba wa kaina horo da kuma sanya juriya a zuciyata. Wato ina nufin bayan horon da ake yi mana a filin wasa, ni a karan kaina ina fita, in yi gudu da dadare da sauran wasanni na motsa jiki masu wahala don in saba wa kaina,” in ji Mane.
Ya ƙara da cewa, “wannan shi ya sa za ka ga in na shiga fili bana gajiya har a tashi. Haka kuma, wannan shi ne dalilin da ya sa ake yi min laƙabi da shahararren ɗan wasan ƙasar Senegal ɗin nan mai suna Sadio Mane, wato ganin irin salon wasanmu ɗaya ne, kai har ma wasu na cewa, wai mun yi kama ko a fuska.”
Sadeeƙ Mane ya bayyana wa Aminya cewa, burinsa shi ne wata rana ya zama kamar Sadio Mane wato ya fita ƙasashe Turai, ya buga wa manyan ƙungiyoyin ƙwallo ƙafa na duniya wasa.
“Kamar kowane matashin ɗan ƙwallo, ni ma babban burina shi ne in buga ƙwallo a ƙasashen Turai, in shahara kamar Sadio Mane. Ina ji a raina wata rana zan buga wa manyan ƙungiyoyi kamar Chealsea da Liɓerpool da Barcelona,” in ji matashi ɗan wasan.
Sai dai Sadeeƙ ya bayyana cewa, ba kamar sauran matasan ’yan ƙwallo ba da suke son shiga Turai gaba-gaɗi, shi yana da burin ya buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars kafin ya tafi ƙasashen Turai da ƙwallo.
“A gaskiya ni in so samu ne, na fi son in fara buga wa Kano Pillars wasa kafin in je Turai. Saboda tunda na taso, ina son Pillars sosai. Haka kuma ina ga a matsayina na ɗan Kano zai zamo abin alfahari a gare ni a ce wata rana na sanya wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillar riga, na ba da tawa gudunmawar,” in ji Mane.
Mane ya bayyana rashin samun haɗuwa da manajan masu ɗaukar matasan ‘yan wasa zuwa ƙasashen Turai, musamman a jihohin Arewa a matsayin wani babban ƙalubale da matasan ‘yan wasa masu hazaƙa ke gamuwa da shi a wannan yanki.
“Babban ƙalubalenmu a nan Kano da sauran jihohin Arewa shi ne wa zai taimake ka, ya haɗa kai da manajan da suke ɗaukar matasan ‘yan wasa zuwa Turai. Ka ga muna da matasa masu ƙwazo da basira sosai, sai dai ba ma samun wannan gatan. Ban san dalilin da ya sa manajojin ɗin ba sa son zuwa nan ba,” In ji Sadeeƙ Mane.