✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙunci ya sa ’yan Arewa buɗa-baki da ruwa zalla a Kalaba

Gaskiya wasu ’yan kasuwar ɓoye kayan suke yi sai sun ga an galabaita sannan su fito da su, su sayar.

A bisa al’ada an saba mai azumi ya yi buɗa-baki da dabino ko kayan marmari irin su lemo da ayaba da kankana da sauransu musamman a tsakanin waɗanda suke zaune a Kudancin ƙasar nan.

Amma saboda sauyin yanayi da ƙunci a yanzu hakan ya fi ƙarfi mutane da yawa musamman ’yan Arewa mazauna garin Kalaba, inda wasu da ruwa kaɗai suke iya buɗe-baki.

Tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki sun sa azumin bana ɗaukar wani salo ba kamar shekarun baya ba, inda abinci musamman kayan marmari ke da rahusa.

Malam Yusha’u Abdullahi wani mai sayar da kayan marmari a Kasuwar Marian da ke Kalaba a hirarsa da Aminiya ya ce abubuwa sun ta’azzara ba kamar da ba.

“Gaskiya cinikin bana sai a hankali musamman yadda masu zuwa sayen kaya kullum sai ƙara raguwa suke yi saboda tsada kaya ga kuma ƙarancin kuɗi a hannunsu.

“Kayan kowane ka taɓa sai ka ji farashinsa ya ƙaru ba kamar yadda aka saba sayensa a baya ba.

“Koyaushe farashin kayan ƙara hauhawa yake yi, yanzu ka ga lemo tun ana sayar da guda ɗaya a kan Naira 50, yanzu Naira 100 muke sayarwa, shi ya sa wasu suka yanke shawara su samu koko ko kunu su sha su haƙura da kayan marmarin,” in ji shi.

Ali Sakkwato shi ma mai sayar da kayan marmarin a garin, ya ce abin na nema ya fi ƙarfinsu.

“Yadda waɗanda muke sayen kayan gare su muke kokawa cewa sun ninka mana farashi haka su ma suke cewa kuɗin sufuri da na jigilar kayan daga wasu jihohin kamar Binuwai da Filato sun ninka saboda ƙarin kuɗin mai.

“Waɗannan na daga cikin ƙorafin da masu sawo kayan ke yi mana.

“Yanzu ka ga dole mu ma mu ƙara farashi saboda za mu shiga mota zuwa kasuwar sayo kayan zuwa da dawowa kuma za mu biya kuɗin dakon kaya ka ga ashe dole ne abubuwa su yi tsada,” in ji shi.

Shi kuwa Saminu Bello da Aminiya ta yi kaciɓis da shi ya zo sayen dabino da abarba a kasuwar, zargin ’yan kasuwar ya yi da ɓoye kayan.

“Gaskiya wasu ’yan kasuwar ɓoye kayan suke yi sai sun ga an galabaita sannan su fito da su, su sayar.

Yanzu ka ga jiya dabino na Naira 100 da na saya ya fi wannan yawa amma yanzu duba fa ka gani ƙwara 4 ne a Naira 100,” in ji shi.

Muhammad Sani wani ɗan kasuwa ya ɗora alhakin haka gaba ɗaya a kan Gwamnatin Tarayya.

“Tun daga lokacin da gwamnati ta janye tallafin man  fetur harkar kasuwanci musamman ga mai ƙaramin ƙarfi ya shiga wani yanayi.

“Shi ya sa yadda muka sawo mu ma haka za mu sayar. Domin babu yadda za a yi ka sayo da tsada kasayar a faɗuwa,” in ji shi.

Yawancin masu zumi suna kokawa da tsadar abin yin buɗa-baki a Kuros Riba ganin cewa mafiya yawa ana kawo ne daga Arewa.