An yi arba tsakanin Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) Ayuba Wabba wanda gwamnan ya sa a kamo ruwa a jallo.
El-Rufai ya sa a kamo Wabba da sauran shugaannin NLC na kasa ne washegarin fara yajin aikin gargadi na kwana biyar da kungiyar ta shiga kan sallamar dubban ma’aikata da gwamnan ke yi.
Jim kadan bayan El-Rufai ya fitar da sanarwar tare da alkawarin tukwici mai tsoka ga wanda ya kawo bayani kan inda shugabannin na NLC suke ne Wabba ya sake jagorantar zanga-zangar lumanar dandazon ’yan kungiyar a garin Kaduna.
A yayin zanga-zangar, Wabba da sauran shugabannin NLC na Kasa sun hadu da gwamnan, tsakaninsu bai fi tazarara mita 100 ba, amma bai uamrci jami’an tsaron da ke tare da shi su kamo su ba.
Ko kafin haduwarsu, Wabba a yayin jawabi ga ’yan jarida ya kalubalnci El-Rufai, “Ya zo ya kama ni, ga mu nan mun fito muna jiransu.”
Yajin aikin da aka farko a ranar Litinin bisa jagorancin Wabba ya tsayar da harkoki a Jihar Kaduna.
’Yan NLC na tattaki a daidai Shataletalen NEPA ne ayarin motocin Gwamna El-Rufai ta wuce ta a daya hannun titin.
Ayarin motocin gwamnan ya je gaban ofishin kamfanin lantarki na KadunaElectric ya tsaya na mintoci, ana kallon-kallo tsakaninsu da ’yan NLC sannan suka wuce ba tare da gwamnan ya sa a kamo mutanen da ya sa a nemo ruwa a jallo ba.