✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zidane ya yi cacar baki da Lucas bazkuez

Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya yi cacar baki tare da dan wasan gabansa Lucas bazkuez jim kadan bayan an tashi wasa a…

Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya yi cacar baki tare da dan wasan gabansa Lucas bazkuez jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin kulob din Athletic Bilbao da na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga ta Sifen a ranar Lahadin da ta wuce.

bazkuez ya nuna bacin ransa a game da yadda Zidane yake yawan ajiye shi a benci da hakan ta sa yake ganin kulob din yake yawan samun rashin nasara ko yin kunnen doki. 

A wasan da Madrid da Atheltic Bilbao suka yi a Lahadin da ta wuce an tashi babu ci ne, wato 0-0 da hakan ya sa kulob din Madrid ya kasance a matsayi na hudu a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar inda kulob din FC Barcelona da ke saman teburin gasar ya ba Madrid tazarar maki 8.

Wasan bai yi wa magoya bayan Madrid dadi ba, ganin yadda kulob din FC Barcelona ya yi kunnen doki da ci 2-2 da kulob din Celta-bigo tun da farko amma na Madrid ya kasa amfani da damar da ya samu wajen rage yawan tazarar maki da ke tsakaninsu.

Lucas bazkuez da ake ganin yaron Zidane ne, sun fara samun sabani ne a kakar wasa ta bana, inda kawo yanzu kocin ya sanya shi a wasanni 6 ne kacal a kakar wasa ta bana, da hakan ba yi masa dadi ba, ta kai suka rika fada wa juna bakaken maganganu.

Rahotanni sun nuna sai da matashin dan kwallon kulob din Dani Cabellos ya shiga tsakani kafin a sasanta kocin da dan kwallon.