Jagoran Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce magoya bayan Ganduje sun shirya tayar da rikici a zaɓen ƙananan hukumomi da ke gudana a Jihar Kano.
Kwankwaso ya bayyana haka ne, jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa da ke Kwankwaso a ƙaramar hukumar Madobi.
- AFCON: CAF ta bai wa Super Eagles maki, ta ci tarar Libya
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An kammala kaɗa ƙuri’a a wasu yankunan Kano
Ya zargi tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da bai wa shugabannin jam’iyyar APC a jihar kuɗi domin su ɗauki ’yan daba don tayar da hankalin jama’a a zaɓen.
“Masu goyon bayan Ganduje na shirin kawo cikas ga zaɓen. Sun bai wa shugabannin jam’iyyarsu kuɗaɗe don su ɗauki motocin haya, kamar Volkswagen Golf, sannan su bai wa mutane makamai domin su farmaki masu zaɓe, su fasa akwatunan zaɓe, su jefa tsoro a zukatan masu jefa ƙuri’a,” in ji Kwankwaso.
Ya kuma ƙara da cewa sun sanar da hukumomi, musamman jami’an tsaro, don su ɗauki matakin da ya dace.
Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayan NNPP da su tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana.
“A halin yanzu, abubuwa suna tafiya daidai, amma mafi yawan waɗanda ke son tayar da hankali za su fito ne da rana zuwa yamma,” Kwankwaso ya bayyana.
Gwamnatin jihar ta ƙudiri aniyar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin duk da cewar rundunar ’yan sandan jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen don bayar da tsaro ba.
Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne saboda wani umarnin kotu da ya hana hukumar zaɓe ta jihar (KANSIEC), damar gudanar da zaɓen.