✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya kashe mutum 2 da mai juna biyu a Enugu

Mutum biyu ne suka mutu ciki akwai mai juna biyu sakamakon bullar zazzabin lassa a jihar Enugu. An dai yi jinkirin kai mai juna biyun…

Mutum biyu ne suka mutu ciki akwai mai juna biyu sakamakon bullar zazzabin lassa a jihar Enugu.

An dai yi jinkirin kai mai juna biyun asibiti bayan ta kamu da cutar, hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

A yanzu haka an samu rahoton bullar cutar da ta kama mutum shida a jihar, an tabbar da mutum uku daga ciki na dauke da cutar.

Ta ukun da aka tabbatar tana dauke da cutar wata budurwa ce mai shekara 24 da ke yin hidimar kasar NYSC a jihar Benuwe, wacce aka dawo da ita gida don yi mata jinya.

Kwamishinar watsa labarai ta jihar Enugu Chidi Aroh, ce ta sanar da hakan yau Juma’a.