An sako tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeria (CBN) Godwin Emefiele daga gidan yarin Kuje bayan sharuddan beli na Naira milian 300.
Emefiele zai yi bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a gida, bayan da ya shafe watanni biyar a tsare kan zarge-zargen da Gwamnatin tarayya take masa kan badakalar Naira biliyan 1.2.
A ranar Asabar ne kakakin Gidan yarin Kuje a tabbatar wa wakilinmu cewa tun ranar Juma’a aka saki Emefeile ya afi gida.
Daya daga cikin lauyoyinsa, Peter Abang ya shaida wa wakilimu cewa an saki tsohon gwamnan CBN din ne domin ya ci gaba da fuskanar shari’a amma ba don ya bar kasar ba.
- Najeriya ba matalauciyar kasa ba ce — Oluremi Tinubu
- An gano asusun banki 593 da Emefiele ya boye kudade a kasashen waje
A ranar 28 ga watan Nuwamba ne Mai Shari’a Hamza Mu’azu na Babbar Kotun Birnin Tarayya ya ba da belin Emefiele bisa sharadin kawo mutum biyu da za su tsaya masa.
Sharadin ya kuma kunshi ajiye Naira miliyan N300 sannan masu tsaya masan su kasance mazaunan Abuja da ke da gidaje a unguwar Maitama.
Alkalin ya kuma umarci Emefiele ya ajiye fasfo dinsa a kotun sannan kada ya bar yankin kwaryar birnin Abuja.
An gurfanar da Emefiele ne a kan zargin laifuka shida na ta’ammali da haramtatun kudade a badakalar sayen motoci na Naira bilian 1.2.