Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, Uba Sani, ya bayya aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron jam’iyyar APC na Jihar, a ranar Talata.
- Yakin Rasha da Ukraine zai haifar da yunwa a duniya –MDD
- An gurfanar da matar da ta raba fetur a wajen biki a gaban kotu
Sanatan ya ce ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar ne don neman hadin kai da goyon baya.
“Na zo na sanar da ku aniyata ta tsayawa takarar Gwamna a APC. Ina bukatar goyon bayanku da tallafinku,” in ji shi.
Kazalika, Sanatan ya jinjina wa Gwamnan Jihar mai ci, Nasir El-Rufa’i kan yadda ya ce ya ciyar da Jihar gaba.
Gwamnan dai yayin wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a kwanakin baya, ya bayyana cewar wanda zai zama Gwamnan Jihar a 2023 na daga cikin jerin mutanensa na kusa-kusa.
“Abin da nake nufi na kusa-kusa, su ne wanda suka yi aiki kafada da kafada da ni tun 2014 wajen hada kan jam’iyya, har zuwa lokacin da muka ci zabe,” inji El-Rufa’i.
Uba Sani dai na daga cikin mutum 11 ’yan gaba-gaban El-Rufa’i, wanda ya faro daga matakin mai bai wa Gwamnan shawara tun daga 2015 zuwa 2019, kafin daga bisani ya sauka ya yi takarar kujerar Sanata.