✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan sayar da kamfanin NNPC idan aka zabe ni – Atiku

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai saida kamfanin man fetur…

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai saida kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da ‘yan kasuwa a jihar Legas a jiya Laraba.

Atiku ya ce, ya taba yunkurin baiwa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo shawarar sayar da kamfanin NNPC amma shugaban bai rattaba hannun amincewar hakan ba.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ce “Zan tabbatar da sayar da NNPC ko da za su kashe ni.”