Wani fitattacen mai sana’ar gyaran baturan mota da ke zaune a garin Jos, fadar Jihar Filato, Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana cewa yana nan yana shirin bude masana’antar yin batir tasa ta kansa a Najeriya.
Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos.
Alhaji Ibrahim Namakaram ya ce wannan sana’a ta gyaran baturan mota da ya fara sama da shekara 33 da suka gabata, ana kawo musu gyaran baturan mota da baturan sola daga wurare daban daban. Kuma ana kawo musu baturan da aka yi amfani da su daga Turai, su saya su tayar da su sannan su sayar.
“Babu shakka mun samu nasarori da dama a cikin wannan sana’a ta gyaran batur. Domin a halin yanzu akwai sama da mutum 70, da suke cin abinci a karkashina. Sannan na samu nasarar bude wuraren yin wannan sana’a har guda biyar a cikin garin Jos. Haka na bude harkar sufurin manyan motoci duk ta dalilin wannan sana’a,’’ inji shi
Ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa masu sana’ar gyaran batur, domin wannan sana’a tana da matukar muhimmanci.