✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaman salama

In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa (Romawa 12:18). Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin KaunarSa da Yake…

In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa (Romawa 12:18).

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin KaunarSa da Yake nuna mana a koyaushe har Ya ba mu wannan zarafi domin mu yi bincike a cikin LittafinSa Mai tsarki a kan zaman salama da juna.

Zaman lafiya kamar yadda muka sani shi ne salama a taKaice. Abu mafi muhimmanci da dan Adam ke bida a yau shi ne zaman lafiya. Zaman lafiya cikin zukatanmu ko cikin iyalanmu ko tsakaninmu da maKwabta ko tsakanin Kasashenmu ko duniya baki daya. Amma a yau ba haka lamarin yake ba, mene ne dalili? Rashin Kauna! Mun bar aikin halin mutumtaka ya shige gaban tafarkin Ubangiji: Galtiyawa 5:19-21 “Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasiKanci da aikin lalata da fajirci da bautar gumaka da sihiri da gaba da jayayya da kishi da fushi da son kai da tsaguwa da hamayya  da hassada da buguwa da shashanci da kuma sauran irinsu. Ina fadakar da ku kamar yadda na fadakar da ku a da cewa masu yin irin wadannan abubuwa, ba za su samu gado a mulkin Allah ba.”

Mulkin Allah na tattare da Kauna da salama da duk albarkar da muka gani cikin Littafi Mai tsarki.

Ko’ina a cikin fadin duniya a yau ana ta fafutikar neman hanyar salama, yau ka ji cewa shugabanin Kasashe za su hallara a waje kaza don a tattauna yadda za a samu zaman lafiya da mafita cikin rayuwar rashin tsaro a duk fadin duniya. A ganinka za a iya yin haka ba tare da bin tafarkin Ubangiji ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko daya, babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah, duk sun baude, sun zama marasa amfani baki daya, babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda daya, maKogwaronsu kamar budadden kabari ne, maganarsu ta yaudara ce masu ciwon baki ne yawan zage-zage da dacin baki gare su, masu hanzarin zub da jini ne, ta ko’ina suka bi sai hallaka da baKin ciki ba su kuma san hanyar salama ba, babu tsoron Allah a cikin sha’aninsu sam.” (Romawa 3:10-18 ko Ishaya 59:8)

Zuciyar mutum na cike da mugunta, idan muka ce za mu nemi zaman salama da wurin ilimin ko basira da ikon kanmu ba tare da bin tafarkin Ubangiji ba, to babu yadda za mu ci nasara. Shi ya sa Ubangiji Allah ya nuna mana cikin maganarSa cewa mu bidi ayyukan ruhu bisa halinmu na mutuntaka domin samun nasara cikin rayuwarmu. Idan mun nemi Ubangiji da dukan zuciyarmu da dukan Karfinmu, babu shakka za mu zama da Kauna irin ta Ubangiji kuma salamarSa za ta kasance tare da mu.

Yau idan muka duba cikin Kasarmu Najeriya, za ka ji wani ya sace kudin Kasa, cin haKKin na Kasa da kai, cin hakin talakawa, cin hakin ma’aikata talakawa (Kasa mai dimbin mutane kusan miliyan dari biyu), me ke kawo irin wannan? Sha’awar kayan duniya da rashin tsoro da Kaunar Allah, ta wurin yin haka ne kuma a kan samu rashin Kauna da maKwabcinka, har ya kai mutum ga rashin samun zaman lafiya cikin rayuwar dan Adam.

Kwanakin nan za mu ga cewa akwai tashe-tsahen hankali a wasu bangarorin Kasar nan da dama, ta wurin nuna bambancin Kabila ko addini ko siyasa da makamantansu. Wannan halin kuwa ya kawo mana rashin salama da juna Kwarai da gaske, kwanan baya a Arewa maso Gabacin Kasar nan an yi ta fama da rashin zaman lafiya har Gwamnatin Tarayya ta sa wata Kungiyar soji don tsaron wannan bangare da a samu zaman lafiya, wanda ake kira “Operation Zaman Lafiya Dole,” domin tsananin irin wannan hali na rashin salama da zaman lafiya ya sa zaman lafiya ta zama “dole!” Zaman lafiya ba abu ne da sai an tilasta maka ba idan kana da Kauna da kuma tsoron Allah a zuciyarka, abu ne mai sauKi idan muka bi tafarkin Ubangiji Allah – mu ji tsoron Sa mu kuma Kaunace Shi da dukan ranmu da Karfinmu, idan har muka yi wannan babu shakka ba za mu samu matsala ba wajen nuna irin wannan hali ga juna.

Sai mu guje wa ayyukan jiki da sha’awace-sha’awace mu nemi albarkar ruhu mai tsarki, domin sha’awar ayyukan jiki ne ke kawo mana rashin salama da zaman lafiya da juna. Littafin Yakubu 4:1-4 na cewa: “Me yake haddasa gaba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku ne suke yaKi da juna a zukatanku ba? Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisan kai. Kukan yi kwadayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da fada. Kukan rasa don ba kwa addu’a ne. Kukan yi addu’a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku batar a kan nishadinku. Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gaba ne da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, ya mai da kansa mai gaba da Allah ke nan.”

A nan mun dai ga hanyar da Ubangiji Ya nuna mana cikin maganarSa, son duniya kan kai mu ga wahala, rashin salama da zaman lafiya kamar yadda muke fuskanta a yau, amma abin farin ciki shi ne, Ubangiji Ya nuna mana mafita; mu nemi albarkar ruhu mai tsarki don tafiyar da rayuwarmu a nan duniya, salamar Ubangiji Allah kuma za ta kasance tare da mu.

Filibiyawa 4:6,7: “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah buKatunku, ta wurin yin addu’a da roKo tare da gode wa Allah.  Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.”

Bari salamar Ubangiji Allah ta kasance cikin zukatanmu, amin.