Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya ce ‘yancin yin addini ba tare da tsangwama ba shi ne ginshikin samun dawwamammiyar zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin addinan Musulunci da na Kirista a Owerri, fadar gwamnatin jihar, inda ya bukaci su mayar da hankali ga abubuwan da za su hada kan mabiyansu ba rabawa ba.
A cewarsa, hakan ce ta sa ya kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin addinan biyu bayan karbar ragamar mulkin jihar domin abubuwa da dama da suka hada su sun fi wadanda suka raba su.
Gwamnan ya kuma ba su tabbacin gwamnatinsa na kiyaye rayuka da dukiyoyin dukkanin mazauna Jihar da kuma bayar da ‘yancin yin addini ga kowa da kowa.
Uzodinma ya kuma yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafin ziyarar ibada ga Kiristocin jihar da kuma na aikin Hajji ga Musulmai.
Ya kara da kira ga shugabannin addinan da su kara jajircewa wajen kauce wa tayar da zaune tsaye.
Da ya ke jawabi yayin gabatar da shugabannin ga gwamnan, mai ba shi shawara kan harkokin addinai, Chidi Nwanebu cewa yayi sun zo ne don kara jaddada matsayinsu na tabbatar da zaman lafiya tare da zama da juna a tsakanin mabiyansu.