✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zama kwararre a hada bidiyon bincike a wata 2

Kwararru a fannin hada fim ne za su ba da horon a aikace, tare da koyar da dabaru da kayan aikin hada bidiyon bincike na…

Ina masu son zama kwararru a fannin aikin jarida na zamani?

To albishirinsu, Media Enterprise Lab, ya shirya bayar da horo mai zurfi kan yadda ake hada bidiyon din bincike.

Gidauniyar Daily Trust tare da hadin Gwiwar Gidauniyar MacArthur sun shirya horon ne ga ’yan jarida da ke da masaniya a fannin bidiyo, amma suke bukatar kwarewa mai zurfi kan yin gajerun bidiyon bincike domin amfanin gidajen talabijin da rediyo da kuma kafofin intanet.

Media Enterprise Lab wata kafa ce da ta daura damarar samar da mafita daga matsalolin da ’yan jarida kan fuskanta bayan sun bar aiki.

Kafar na yin hakan ne ta hanyar ba su horo mai zurfi da dabarun aikin jarida na zamani da kuma karfafa su su zama masu dogaro da kansu, ko yin aikin jaridar zamani na wucin gadi da sauransu, bayan sun bar aiki.

Horon na wata biyu ne, kuma ya kunshi yin abubuwa a aikace tare da  koya wa mahalarta rukunnan shirya fim, kamar dabarun kirkiro labari, sarrafa kyamara, tsara haske da sauti, da tace bidiyo.

Kwararru a fannin hada fim ne za su ba da horon, kuma a aikace, sannan za su koya wa mahalarta dabaru da kayan aikin hada bidiyon bincike na zamani.

Media Enterprise Lab ya tsara wannan horo ne domin koya dabaru da kuma hanyoyin samun kudaden shiga daga aikinsu.

Ga masu neman shiga, sai su latsa nan, su cike takardun da suka kamata.

Za a bayar da horon ne a kan garabasa, amma kowane mahalarci zai biya N50,000 na rajista da kayan karatu da kuma takardar shaidar kwarewa.

Za a fara horon ne a cikin mako na uku na watan Nuwamba, 2022.

Domin karin bayani sai a nemi Immam Shuaib a kan 08065931928, ko Ele Ifah Sunday a kan 07037282675, ko kuma a tura sakon imel zuwa [email protected].