✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake fitar da Zakkar Kono

Bayanin yadda za ku fitar da Zakatul Fidr a cikin sauki

A yayin da watan Ramadan din wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali.

Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.”

Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abun da za su ci a lokacin Karamar Sallah.

Yadda ake fitarwa

Mutum zai fitar wa kansa da kuma wadanda yake ciyarwa kamar mata, ’ya’ya da ma’aikata da sauransu idan Musulmai ne.

“Manzon Allah Ya wajabta fitar da zakkar kono ga babba da yaro, ’yantacce da bawa, daga cikin wadanda kuke ciyarwa,” kamar yadda Abdullahi bn Umar ya ruwaito a Hadisi.

Mai fitar da zakkar zai fara ne da fitar wa kansa, sannan sauran mutanen gwargwadon wajibcin ciyar da su a kansa.

Adadin da ake fitarwa

Kowanne mutum daya za a fitar masa da Sa’i daya, wato Mudun Nabi hudu.

Idan babu Sa’i ko Mudun Nabin awo, ana iya aunawa da hannu.

Malamai sun ce Mudun Nabi daya daidai yake da cikin tafin hannu biyu na matsakaicin mutum.

Abin da ake fitarwa

Ana fitar da zakkar kono ce daga nau’in danyen abincin mutanen garin.

Ana fitarwa ne daga abin da ya karu a kan abincin rana da yinin mai fitarwa da iyalansa a lokacin.

Lokacin fitarwa

Malamai sun bayyana cewa ya halatta a fitar da zakkar tun daga ranar 28 ga Ramadan.

Hadisi ya nuna, “Abauullahi bn Abbas kan ba da ita da kwana daya ko kwana biyu kafin ranar Sallah.”

Amma tana wajaba ne daga safiyar ranar Karamar Sallah, a kuma gama kafin Sallar Idi.

“Wanda ya bayar kafin sallah to zakka ce karbabbiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma to sadaka ya bayar kamar sauran sadakoki.”

Malamai sun ce haramun ne a jinkirta fitar da da ita ba tare da uzuri ba.

 Wadanda ake ba wa

Hadisi ya nuna miskinai ake bai wa.

Wasu malamai na ganin ana iya ba da ita ga sauran mutanen da ake ba wa zakkar farilla (bayi, matafiya, masu bashi a kansu, masu aikin karbar zakka, masu aikin fisabilillahi, wadanda ake kwadayin su musuluntar).

Wanda aka ba wa zakkar shi ma zai fitar, idan har an samu ragowa.