✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakarun Kulob na Turai: Barcelona ta kafa sabon tarihi

A shekaranjiya Laraba ne kulob din FC Barcelona na Sifen ya kafa sabon tarihi bayan ya lallasa na Paris Saint Germain (PSG) na Faransa a…

A shekaranjiya Laraba ne kulob din FC Barcelona na Sifen ya kafa sabon tarihi bayan ya lallasa na Paris Saint Germain (PSG) na Faransa a wasa zagaye na biyu da ci 6-1 da hakan ya sa kulob din ya haye matakin kwata-fainal a gasar zakarun Turai (Champions League).
Idan za a tuna, kimanin makwanni uku da suka wuce ne kulob din PSG ya lallasa na Barcelona a Faransa da ci 4-0 amma abin mamaki sai ga shi a wasa zagaye na biyu Barcelona ta fanshe, har ma ta kara inda aka tashi wasa 6-1.
Wannan ya nuna Barcelona ta kafa sabon tarihi a gasar, ganin cewa shi ne kulob na farko da aka taba doke wa da kwallaye hudu a wasan zagaye na farko amma ya farfado a wasa zagaye na biyu da ci 6-1.
Da yawa daga cikin masoya kwallon kafa sun dauka za a fitar da FC Barcelona daga gasar, musamman ganin yadda kwallaye suka yi yawa a wasan farko, amma sai ga shi sun ba marada kunya.
’Yan kwallon FC Barcelona Luis Suarez da Lionel Messi da Neymar da Sergi Roberto ne suka zura kwallayen da suka ba kulob din su damar doke na PSG.  Yayin da Edinson Cabani ne ya zura kwallo daya da PSG ta zura a ragar Barcelona.
Kawo yanzu kulob hudu ne suka haye matakin Kwata-Fainal da suka hada da Bayern Munich na Jamus da Real Madrid da FC Barcelona daga Sifen da kuma Borussia Dortmund na Jamus.
A makon gobe ne sauran kungiyoyi takwas za su yi nasu wasan a zagaye na biyu don a tantance hudun da za su haye matakin kwata-fainal.