Jam’iyyar NNPP ta ce har yanzu Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ba ta damka wa lauyoyinta ainihin kundin hukuncin kotun da ta kwace kujerar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ba.
NNPP ta yi korafin cewa jinkirin fitar da ainihin takardar hukuncin na barazana ga kokarin jam’iyyar na dawo da kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf da kotu ta kwace.
Tun a ranar Juma’a da kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kwace kujerar Abba, gwamnan ya yi alkawarin daukaka kara zuwa Kotun Koli tare da kiran magoya bayansa da kada su yanke kauna daga bangaren shari’a.
Sai dai yanzu bayan kwanaki hudu, shugabancin NNPP na kokawa cewa har yanzu ba a ba wa lauyoyinsu ainihin kwafin hukuncin kotun daukaka karar ba, ballantana su fara aikin tafiya Kotun Koli.
- Makiyan Kwankwaso ke neman a kwace kujerata —Abba
- Shin Hukuncin Kotuna Kan Zaben Gwamnoni Ya Sauya Dimokariɗiyya?
Mukaddashin shugaban NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ne ya yi wannan korafi a ranar Litinin yana mai cewa rashin ba su kundin hukuncin kotun ya fara shiga kwanaki 14 da doka ta kayyade da za su iya daukaka karar.
“Abin takaici, wannan yanayi na haifar da zargi an shirya jefa jam’iyyarmu da kuma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma lauyoyinmu cikin damuwa a yayin da lauyoyinmu ke aikin daukaka kara domin samun adalci a gaban Kotun Koli,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gargadi cewa za ta sa kafar wanda da magoya bayan jam’iyyu da suka yi yunkurin gudanar da kowace irin zanga-zanga a jihar kan hukuncin kotun daukaka karar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya gargadi masu neman shirya zanga-zanga ko tatttakin a jihar kan hukuncin kotun da cewa duk wanda runduna ta samu yana karya doka a jihar, zai yaba wa aya zaki.
Kakakin rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce gargadin yana da muhimmanci saboda rahotannin da suka samu kan yadda magoya bayan wata jami’iyya ke amfani da wasu hanyoyiyn bayan fage wajen kiran jama’a da su fito kan titunan Kano domin zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka karar.
Kiyawa ya ce, “Mun samu rahoton shirin masu zanga-zangar na tsayar da harkoki da ma tayar da hankali a Kano, shi ya sa muke gargadin jama’a da su yi hattara; Duk wanda zai yi zanga-zanga to ya wajibi ne ya yi a bisa yadda doka ta tsara.
“Sannan a sani cewa ranar Alhamsi, 16 ga Nuwamba, 2023, jajibirin zaman kotun daukaka karar, rundunarmu ta yi zama da shugabannin jam’iyyun NNPP da APC inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya,” a Kano, duk yadda hukuncin kotun ya kasance.
“Sun amince a hana kowane irin taron siyasa, sannan magoya bayansu ba za su yi kowane irin abu mai alaka da zanga-zanga ko tattaki ko biki ko lafazi da zai iya tunzura jama’a ko jawo martani ko wata matsalar tsaro ko cin mutuncin bangaren shari’a ba.”