✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: Abba ya gabatar da shaidu 241

Dan takarar Gwamna Jihar Kano a Jam’iyyar PDP a zaben bana, Injiniya Abba K. Yusuf, ya gabatar da shaidu 241 a gaban Kotun Kararrakin Zabe…

Dan takarar Gwamna Jihar Kano a Jam’iyyar PDP a zaben bana, Injiniya Abba K. Yusuf, ya gabatar da shaidu 241 a gaban Kotun Kararrakin Zabe ta Jihar domin gamsar da ita cewa ba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya lashe zaben ba.

Abba Yusuf, wanda Hukumar INEC ta ce ya sha kaye a hannun Gwamna Ganduje a zaben da aka yi, masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna zargin an tafka magudi, zargin da Jam’iyyar APC da  Hukumar INEC suka musanta.

Lauyan masu kara Adeboyega Awomolo (SAN)wanda shi ne ya gabatar da  shaidun a gaban kotun ya ce za su yi kokari su kara tattara wasu shaidun domin gamsar da kotun, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Mista Awomolo ya bayyana wa kotun cewa cikin shaidar da ya gabatar akwai sahihan sakamakon zabe na mazabun kananan hukumomin Albasu da Bebeji da Bichi da Dambatta da Garun Malam da Gwarzo da Karaye da Kura da Madobi da Nasarawa da Rano da Rogo da Sumaila da Tudun Wada da kuma Warawa da sauransu.

Sai dai lauyoyin da ke kare Gwamna Ganduje da Jam’iyyar APC, Offiong Offiong da Ahmad Raji (SAN) sun yi watsi da shaidun da aka gabatar.

Mista Offiong ya bayyana cewa “Masu karar ba su fito da shaidun karara muka gani ba, jakunkuna kawai aka kawo, muna so mu ga asalin abubuwan da ke cikin jakunkunan.’’

Sai dai Mai shari’a Halima Shamaki ta yi watsi da bukatar da Mista Offiong ya gabatar, inda ta amince da takardun sakamakon zaben a matsayin shaida.

Ana sa ran shaidu kusan 785 za su hallara a gaban kotu domin bayar da shaida daga bangarorin APC da PDP kan zaben Gwamnan da aka gudanar a watan Maris din da ya gabata.

Abba Kabir Yusuf da Jam’iyyar PDP ne suka shigar da karar bisa zargin cewa zaben cike yake da magudi da kuma aika-aikar ’yan bangar siyasa. Kuma masu karar sun bukaci kotu ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi, a zagaye na biyu, bisa zargin cewa babu tsarin rashin kammaluwar zabe a cikin dokar zabe.

Hukumar INEC da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun musanta zarge-zargen na PDP.

Kotun dai tana da kwana 180 don ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar a ranar 11 ga watan Afrilun bana.