Wata kungiyar mambobin jam’iyyar APC a jihar Kano karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga sun yi kira ga Babban Ofishin jam’iyyar na kasa da ya kafa kwamiti na rikon kwarya da zai jagoranci jam’iyyar a jihar.
A wata tattauna wa da ya yi da manema labarai, Mairiga ya zargi Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da rashin iya shugabanci kuma ya gaza dinke barakar jam’iyyar.
- Majalisar Kano ta amince Ganduje ya karbo bashin N20bn
- PDP ta kaurace wa zaben kananan hukumomin Kano
- An yi gwajin sabon irinn wake a Kano
- Dan takara ya yi martani ga zanga-zangar kin sa a Kano
“Ko da yake Abdullahi Abbas ya zama shugaba ne ta hanyar kurda-kurda, a maimakon ya dinke barakar dake tsakaninsa da mutane sai yake neman kara tada wata fitinar, in ji Mairiga.
A yayin tattaunawarsa da manema labarai a Kano, Mairiga ya ce yana magana ne da yawun kungiyar Legacy Group; mambobin rusasshiyar ANPP, CPC da ANC, tun a 2014 kafin gudanar da zaben 2015.
Ya ci gaba da zargin Abdullahi Abbas da rashin iya shugabanci, wanda ya sabawa doka da oda wanda a cewarsa dukkanin abin da ya sabawa ra’ayinsu to bashi da amfani.
Mairiga ya kara jan hankalin ‘yan takarar kananan hukumomin da za su fafata a zaben da za a gudanar a watan Janairun 2021a kan muddin suka bi tsarin Abdullahi Abbas to kuwa tabbas sun yi a banza.
Mairiga, tsohon mataimaki na musamman ga Sanata Ibrahim Shekarau a lokacin da yake gwamnan jihar Kano, ya yi kira ga Babban Ofishin jam’iyyar APC da ke Abuja da ya samar da wani shugaban rikon kwarya wanda a cewarsa rashin yin hakan ka iya haifar da rugujewar jam’iyyar a 2023.
Aminiya ta ruwaito cewa babu wata jituwa tsakanin Legacy Group da kuma tsagin shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas, wanda na hannun daman gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ne.
Kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar, Abbas, ya ci tura domin a lokacin hada wannan rahoton an kasa samunsa a waya.