✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben gobe: Jihar Kaduna na bukatar addu’a

A gobe Asabar ce insha Allahu za a gudanar da zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi 29 daga cikin 36 da ake da su a kasar…

A gobe Asabar ce insha Allahu za a gudanar da zaben gwamnoni da wakilan majalisun jihohi 29 daga cikin 36 da ake da su a kasar nan, wanda zai kawo zagaye na karshe bayan zaben Shugaban Kasa da wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa da aka yi makonni biyu da suka gabata. Sai dai kuma ga dukkan alamu hankalin jama’a ya fi karkata ne ga zaben Gwamna da za a yi a Jihar Kaduna saboda yanayin ’yan takarar da jam’iyyun APC da PDP suka tsayar.

Ita dai Jam’iyyar APC ta tsayar da Gwamna mai ci Nasir Ahmad El-Rufa’i ne a matsayin dan takararta da kuma Khadija Balarabe a matsayin mataimakiyarsa, a yayin da Jam’iyyar PDP ta tsayar da Isa Muhammad Ashiru a matsayin dan takararta da Sunday Marshal Katung a matsayin wanda zai taimaka masa.

Kasancewar mataimakiyar El-Rufa’i Khadija Balarabe Musulma ce daga yankin Kudancin Kaduna, hakan ya haifar da cece-ku-ce, musamman daga yankin Kudancin Kaduna inda wadansu ke ganin duk da cewa Khadija Balarabe ’yar asalin yankin ne amma an nuna masu wariya a addinance. Zargin da Gwamna El-Rufa’i ya karyata, inda ya nuna cewa so yake a rika la’akari da cancanta ba addini ba a duk lokacin da za a nada wani mutum a kan wani mukami.

Wannan mataki da Gwamna El-Rufa’i ya dauka ya sanya Jihar Kaduna, musamman Kudancin Kaduna ta dauki zafi, domin daga abubuwan da suke fitowa a kafafen watsa labarai da kafafen sada zumunta za a fahimci cewa lallai zaben da za a yi a Jihar Kaduna zai dauki sabon salo, wanda ya sanya jihar  take bukatar addu’a domin a yi zaben lafiya a kare lafiya ba tare da wani ya samu ko kwarzane ba.

Tun bayan da aka kammala zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa magoya bayan jam’iyyun siyasu da shugabannin addini suke ta kartar kasa suna nuna dan takarar da suke ganin shi ne jama’ar Kaduna ya dace su zaba. Abin tsoron shi ne yadda ake tayar da jijiyoyin wuya wurin tallata dan takara, tun ba ma a kafofin yada labarai na sada zumunta ba.

A duk lokacin da aka sanya harkar addini a cikin wata harka to ba a daukar wannan al’amarin da wasa domin akan yi shi ne bakin rai bakin fama. Wannan ne ya sanya tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ahmed Makarfi ya fito ta kafar watsa labarai yana jan hankalin shugabannin addini su yi taka-tsantsan kada su jefa Jihar Kaduna a irin mawuyacin halin da ta shiga shekara 19 da suka gabata (lokacin da aka yi batun jaddada shari’a ke nan) wanda har yanzu ba ta fita daga ciki ba. Ya ce ya kamata a bar kowa ya zabi jam’iyyar da yake so, yadda za a yi zabe lafiya a gama lafiya ba tare da dan Kudancin Kaduna yana jin tsoron zuwa Arewacin Kaduna ba, ko dan Arewacin Kaduna yana jin tsoron zuwa Kudancin Kaduna ba.

Abin tsoron shi ne kada rikici ya tashi a lokacin zaben na Gwamnan Kaduna, ko kuma bayan zaben wato a lokacin da aka bayyana sakamakon zaben. Domin wadansu ba za su iya jurewa ba idan dan takararsu ya fadi zabe kuma wadansu suka rika nuna farin cikinsu a gabansu. A wani lokacin kuma masu murnar ne za su harzuka wadanda dan takararsu ya fadi har ta kai ga an tayar da husuma. Haka kuma kalaman da shugabannin addini suke yi, musamman a wani bangare na jihar suna iya harzuka mabiyansu su tayar da rikici idan dan takarar da suke so ya fadi zabe.

Saboda haka akwai bukatar a dauki kwararan matakan tsaro a lokacin zaben da kuma bayan an kammala zaben, sannan idan zai yiwu a dauki matakin hana yadda ake yin murna idan an samu nasara a zabe, wato yadda matasa suke yin ganganci da ababen hawa suna jikkata kawunansu da sauran mutane masu kallo. Domin a irin haka ne ake tabo wani wanda dan takararsa bai yi nasara ba, shi kuma sai ya kasa hakuri ya ce zai dauki fansa, daga nan sai al’amura su lalace rikici ya tashi har ya watsu a sauran wurare.

Matasa ku kula kada ku yarda ’yan siyaya su zuga ku har ku tayar da fitina, domin fitina mayar da kasa baya take yi, kuma ku ne manyan gobe, idan kuka taimaka kasar ta ruguje za ku yi kuka da idonku nan gaba. Su kuma ’yan siyasa su rika taka-tsantsan game da kalaman da suke furtawa, domin idan jihar babu zaman lafiya ko sun ci zaben ba za su ji dadin mulkinta ba.

Ita kuma Hukumar Zabe (INEC) ta tabbatar ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci wanda zai zama karbabbe ga kowa, ta haka ne za a samu zaman lafiya a yayin zabe da kuma bayansa.

Muna rokon Allah Ya sanya a yi zabe lafiya a Jihar Kaduna da sauran jihohi, muna kuma fata a fadi sakamako lafiya ba tare da wadansu sun harzuka wadansu har su tayar da fitinar da za ta iya jawo rasa rayuka da asarar dukiyoyi ba.

Yadda Jihar Kaduna ta dauki zafi akwai bukatar kowa da kowa ya himmatu wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin zabe da  bayansa a Jihar Kaduna, domin babu abin da ya gagari Allah. Allah Ya taimaka a yi zaben lafiya.