Sakamakon zaben gwamnan da hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar zuwa yanzu ya nuna cewa jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar Edo ta lashe kananan hukumomi 11, yayin da jam’iyyar adawa ta APC ta yi nasara a kananan hukumomi biyar.
Yayin da ake jiran sakamakon kananan hukumomi biyu, PDP na da kuri’u 243,606, ita kuma APC tana da kuri’u 144,955.
Hakan na nufin PDP ta bai wa APC tazarar kuri’u 98,651.
Sai dai kuma akwai takaddama a kan wannan sakamako bayan da wakilin PDP a wajen tattara sakamakon, dan Majalisar Wakilai Ogbeide Ihama, ya nuna rashin amincewa da shi.
A cewarsa, an samu aringizon kuri’u da satar akwatin zabe a wasu wurare, amma ba a soke sakamakon ba kamar yadda aka yi a wasu wuraren.
Ya yi kira ga hukumar INEC ta dauki mataki kamar yadda aka yi a sauran wurare inda aka samu matsaloli irin wannan.
Ga dai yadda sakamakon yake a kananan hukumomin da aka bayyana:
Etsako ta Yamma
PDP 17,959
APC 26,140
Esan ta Kudu Maso Gabas
PDP 10,563
APC 9,237
Oredo
APC 18,361
PDP 63,498
Esan ta Yamma
APC 7,189
PDP 17,434
Igueben
APC 5,199
PDP 10,22
Esan ta Tsakiya
APC 6, 719
PDP 10,694
Esan ta Arewa Maso Gabas
APC 6, 556
PDP 13579
Ikpoba Okha
APC 18,218
PDP 4,030
Uhunmwonde
APC 5,972
PDP 10,022
Egor
APC 10,202
PDP 27,621
Owan ta Gabas
APC 19,295
PDP 14,762
Owan ta Yamma
APC 11,193
PDP 11,485
Ovia ta Arewa Maso Gabas
APC 9,907
PDP 16,987
Akoko-Edo
APC 22,963
PDP 20,101
Etsako ta Gabas
APC 17,011
PDP 10,668
Etsako ta Tsakiya
APC 8,359
PDP 7,478
Kanan hukumomin da ba a bayyana sakamakonsu ba su ne Orhionmwon da Ovia ta Kudu Maso Yamma.