Gwamnatin Birtaniya ta yi barazanar sa takunkumi ga masu tayar da fitina a zaben gwamnan jihohin Edo da Ondo da ke tafe.
Ofishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya wanda ya ce yana lura da abubuwan da ke wakana gabanin zabukan da ke kara karatowa, ya kuma ce ba zai yi wata-wata ba wajen daukar mataki kan masu tayar da fitina.
- Amurka ta haramta kayan China kan musguna wa Musulmi
- Amurka ta sa wa masu magudin zabe a Najeriya takunkumi
- Yara 10 sun kone kurmus a gobarar makaranta
“Birtaniya ba ta daukar rikicin siyasa da wasa kamar yadda ta yi a babban zaben 2019, kuma za ta ci gaba da daukar mataki kan mutanen da muka gano suna da hannu a rikici a lokutan zabe.
“Wannan ya shafi hana izinin shiga Birtaniya da hana amfani da kadarori da ke Birtaniya da kuma gurfanarwa karkashin dokokin kasa da kasa”, inji Ofishin jakadancin Birtaniya.
Sanarwar na zuwa ne washegarin ranar da Amurka ta sanar da sanya takunkumi ga masu hannu a rikicin zaben Jihohin Kogi da Bayelsa na watan Nuwamban 2019 da na jihohi biyun da ke tafe.
Ofishin Jakadancin Birtaniya ya ce zabukan na da muhimmanci ga samar da shugabanci na gari a jihohin da kuma karfafa dimokuradiyya a Najeriya.
Ta kuma yi na’am da yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin da ke cikin zaben suka rattaba hannu a kai, tare da kira ga hukumar zabe (INEC) da ‘yan sanda da sauran hukumomi su tabbatar da zabe mai inganci.
“Hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da zabukan ke kara matsowa”, inji sanarwar.