✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Bayelsa: APC ba ta da dan takarar Gwamnan jihar – Kotu

Saura kwana biyu kacal a gudanar da zaben Gwamnan jihar Bayelsa, wata babbar kotun tarayya ta Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Ta soke takarar dan…

Saura kwana biyu kacal a gudanar da zaben Gwamnan jihar Bayelsa, wata babbar kotun tarayya ta Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Ta soke takarar dan takarar Gwamna karkashin jam’iyyar APC a jihar.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a safiyar yau Alhamis.

Wannan na nufin jam’iyyar APC mai mulkin kasar ba ta da dan takarar gwamna a zaben jihar da za a yi ranar Asabar.

Mai shari’a Jane Inyang ya ce David Lyon bai bi dokokin tsarin mulki ba wajen zaben fitar da gwani na jam’iyyar da aka yi ba.