Nze Akachukwu Nwakpo na jam’iyyar ADC, daya daga cikin ’yan takara a zaben gwamnan Jihar Anambra, ya jefa wa Farfesa Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA kuri’arsa.
Nwakpo ya jefa wa Soludo kuri’arsa a karashen zaben gwamnan Jihar Anambra da ake gudanarwa ranar Talata a Karamar Hukumar Ihiala.
Zaben da aka gudanar da shi a ranar Asabar, Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana cewa bai kammala ba sakamakon tangardar da aka fuskanta ta matsalar tsaro.
Da yake zanta wa da manema labarai bayan kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba ta 004 a Unguwar Okija da ke Karamar Hukumar Ihiala, Nwakpo ya ce ya yanke shawarar hakan ce bayan tuntuba da kuma tattaunawar tsanaki da matasan Karamar Hukumar.
A cewarsa, wannan shawara ta biyo bayan ganin cewa jam’iyyarsa ta ADC ba za ta kai labari.
Haka kuma, Nwakpo ya ce ya yi hakan ne saboda hangen cewa jam’iyyar APGA tana da dama ta kashi 90 cikin 100 na samun nasarar lashe zaben, lamarin da ya gwammace ya jefa mata kuri’a madadin ya yi asara.
Yayin da manema labarai suka tuntube shi ko ya yi hakan ne da goyon bayan jam’iyyarsa ta ADC, Nwankpo ya ce shawara ce ta kashin kansa domin ya samu shiga a gwamnatin jam’iyyar APGA mai ci a yanzu karkashin jagorancin Gwamna Willie Obiano.
Ya yaba wa jam’ian tsaro saboda jajircewarsu da tsayin daka da suka yi wajen tabbatar da tsaro mai inganci a lokacin zaben da kuma bayansa.