✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Amurka: Na lashe zabe amma zan garzaya kotu —Trump

Yayin da ake tsaka da kriga kuri’un zaben Shugaban Kasar Amurka kafin a sanar da sakamakon zaben, Shugaban kasar, Donald Trump mai neman tazarce ya…

Yayin da ake tsaka da kriga kuri’un zaben Shugaban Kasar Amurka kafin a sanar da sakamakon zaben, Shugaban kasar, Donald Trump mai neman tazarce ya yi ikirarin lashe zaben amma zai garzaya kotun koli domin kalubalantar yadda kidayar kuri’u ta gudana.

Trump ya bayyana haka ne a dakin taro na ‘East Room’ da ke fadar White House, inda ya ce, “Mun lashe wannan zaben.

“Wannan murdiya ce ga al’ummar kasar Amurka”, kamar yadda Trump ya bayyana.

Trump dan takarar jam’iyyar ‘Republican’ yana karawa ne da Joe Biden dan takarar jam’iyyar ‘Democrat’, wanda sakamakon kidayar kuri’un ke nuna suna tafiya kusan kunnen doki.

Trump ya bukaci da a dakatar da karbar sakamkon kidayar kuri’un da aka kada ta yanar-gizo, saboda rashin zuwan wasu daga ciki a kan lokaci.

Bayani na nan tafe.