Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta jaddada cewa babu wani dan takara ko jam’iyya da za ta mara wa baya a zaben 2023 mai karatowa.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce babu wani abu a gaban hukumar da ya wuce tsare-taren zabe.
- Rikici ya kunno kai tsakanin masarautar Hausawa da ta Zabarmawa a Legas
- Yadda mahara suka kona wani coci
“INEC ba jam’iyya ba ce, ba ta da dan takara a zaben. Abin da muka sa Baga bai wuce tsare-tsaren zabe ba.”
Ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa wasu jami’an da INEC ta nada (SPOs) don aikin zabe mai zuwa jawabi a Abuja.
A cewarsa, “Hukumar na da yakinin gudanar da zabe mafi inganci a 2023, kuma ku ne mutanen da za ku taimaka wa hukumar wajen cim ma nasarar hakan.
Yakubu ya bayyana aikin jami’an a matsayin mai matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasara a zaben na 2023.
Don haka ya yi kira a gare su da su tsare gaskiya da mutunci yayin zaben.
(NAN)