Ka ce: “Ya Allah Mamallakin mulki. Kana bayar da mulki ga wanda Kake so, Kana zare mulki ga wanda Kake so, kuma Kana kaskantar da wanda Kake so, ga hannunKa alheri yake. Lallai ne Kai a kan kowane abu Mai ikon yi ne.” Allah Ya yi gaskiya, Aya ta 26 a Suratul Al-Imrana ke nan a cikin Alkur`an mai tsarki.
Abin da ya sa na fara da wannan aya ta sama bai wuce irin halin da kasar nan ta fara shiga ba, daga yunkurin mazajen da suke ha-maza-ha- mata, sai sun mallake ta a zabubbukan shekarar 2015, idan Allah Ya kai mu, bisa ga karatowar zabubbukan da wasu suke ganin daga ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, an yi rabin shekaru hudu na masu mulkin da aka zaba irinsu shugaban kasa da gwamnonin jihohi da `yan Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi, don haka daga wancan rana a cikin irin wannan shekara yakin neman zabe zai fara kankama, don masu iya magana kan ce “Da safe ake kama fara” ko kuma “ Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka.”
Alal misali, yunkurin da jam`iyyun adawa na ANPP da ACN da CPC suke yi na hadewa wuri guda da aniyar su kafa sabuwar jam`iyyar APC, (wanda tuni tafiya don tabbatuwar hakan ta yi nisa), duk suna yi ne da su ga lallai, idan lokacin ya yi sun karbe mulki daga hannun jam`iyyar PDP, wadda tun da aka fara mulkin jamhuriya ta hudu, ita take mulki a gwamnatin tsakiya (in kuma an bi ta hasashen tsohon shugaban jam`iyyar PDP din na kasa baki daya Yarima bincent Ogbulafor, to har yanzu tana da sauran wa`adin shekaru 46, daga cikin 60 din da ya diba mata), bayan mulkin gwamnatin tsakiyar, ita kuma ke da mafi rinjayen gwamnonin jihohi da na mambobin `yan Majalisun Dokoki na kasa.
A gefe daya kuma ita kanta jam`iyyar PDP din danfare take da rigingimu iri-iri, da wasu ma in ka ji su sai ka ga tamkar zai yi matukar wahalar ta samu warware su, har kuma ta iya tunkarar babban zaben shekarar 2015, amma ai dama masu iya magana kan ce “Wai babba juji ne,” wasu kuma na cewa “Wai karbuwa da karfin da jam`iyyar ta PDP ta yi ya sa ake ta wannan rikici a cikinta. Sannan kuma a gefe daya ga rashin dimokuradiyyar cikin gida da suka yi kace-kace a cikin jam`iyyun kasar nan kar dai ka ce jam`iyyar PDP.
Misali, yanzu dauki rikicin zaben kungiyar gwamnonin kasar nan, inda gwamnoni 19 suka taru suka sake zaben gwamnan Jihar Ribas Mista Rotimi Amaechi a karo na biyu. Amma kuma, wasu gwamnoni 16, suka koma gefe daya suka ce ba shi aka zaba ba, wai gwamnan jihar Filato Mista Dabid Jonah Jang aka zaba. Wannan rikici da gwamnonin PDP suka jefa ta, ya zuwa yanzu har ya kai gwamnan Jihar Bauchi Malam Isah Yuguda, daya daga cikin `yan takarar wancan mukami da ya janye daf da za a kada kuri`a kuma mai goyon bayan zaben da aka ce an yi wa gwamnan na Jihar Filato, yanzu ya ba da shelar cewa haihata-haihata ba ya kara halartar taron kungiyar Gwamnonin Arewa, bisa ga abin da ya kira munafucin da takwarorinsa suka yi a kan zaben, amma shi ko me ya yi wa jam`iyyar ANPP, wadda ta tsayar da shi zaben gwamnan jihar, amma bayan ya yi nasara ya koma cikin tsohuwar jam`iyyarsa ta PDP da ta hana shi takarar?
`Yan kasa suna ganin duk wannan rikici ba zai rasa nasaba da zabubbukan 2015 ba, a cikin jam`iyyar ta PDP, inda masu goyon bayan gwamnan Jihar Ribas su ake yi wa kallon masu goyon bayan takarar neman shugaban kasar Alhaji Sule Lamido da Gwamnan Ribas, yayin da dayan bangaren ake masa kallon maso goyon bayan sake takarar shugaba Jonathan, a inuwar jam`iyyar PDP.
A nawa tsinkayen, tarihin akasarin wadanda suka samu mulkin kasar nan tun da aka fara wannan mulki na dimokuradiyya yau shekaru 14, kusan a bagas suka same shi. Bari mu fara da irin yadda aka sako Cif Olusegun Obasanjo daga gidan sarka yana zaman daurin rai-da-rai, ya zarce fadar shugaban kasa a zaman shugaban kasar nan. Da kuma irin yadda shi kuma ya yi watsi da wadanda suka yi sanadiyar zuwansa kan karagar mulkin, ya je ya lalubo marigayi shugaba Umaru Musa `Yar`aduwa da Shugaba Jonathan a shekarar 2007, ya mika masu takara, alhali ga mazajen da ke gabansa, wadanda kuma suka nuna suna matukar kwadayin su gaje shi.
Idan ka komo akan mukaman gwamnonin jihohi, ka fara da Jihar Sakkwato, inda Gwamna Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako yake mataimakin Gwamna Alhaji Attahir dalhatu Bafarawa kusan tsawon shekaru bakwai a inuwar jam`iyyar ANPP, amma rikicin ka da Alhaji Aliyu Wammako ya gaje shi ya hada su, Gwamna Bafarawa ya nemi Majalisar Dokokin jihar ta tsige shi (Wammako), amma Allah Ya taimake shi ya sauka, ya yi takara a jam`iyyar PDP, ya kuma kai ga nasara, abin da ya sa Gwamna Bafarawa yana so baya so dole a shekarar 2007 ya mika ragamar mulki ga Gwamna Wammako.
Haka irin wannan labarin yake a Jihar Bauchi tsakanin Gwamna Adamu Mu`azu da Gwamna Malam Isah Yuguda. Kowa ya sani cewa gwamna Malam Isah Yuguda ya yi Minista har karo biyu a wannan jamhuriyar a matsayin mai wakiltar jiharsa ta Bauchi, amma fadin yana neman ya gaji Gwamna Adamu Mu`azu a shekarar 2007 ta sanya Gwamna Adamu Mu`azu ya ce Malam Isah din ba ma dan asalin jihar ba ne, amma dai cikin ikon Allah shi ya gaji Alhaji Adamu Mu`azu.
Irin wadannan misalai sunanan bila`adadin a cikin wannan jamhuriya ta hudu, baya ga irin yadda su Gwamna Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema da Dokta Ma`azu Babangida Aliyu na Jihar Neja da Malam Ibrahim Shekarau na Jihar Kano da Alhaji Sule Lamido na Jihar Jigawa, wadanda rashin fili ba zai bar ni in kawo tarihin yadda suka samu kansu a karagar mulki a wannan jamhuriya ba. Don haka nake ganin duk mai neman mulki a shekarar 2015 da ma gaba, to, ya nema wurin Allah. Allah Ka ba mu ikon zaben shugabanni nagari, amin.
Zaben 2015: A nemi mulki wurin Allah
Ka ce: “Ya Allah Mamallakin mulki. Kana bayar da mulki ga wanda Kake so, Kana zare mulki ga wanda Kake so, kuma Kana kaskantar da…