✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zababbun tambayoyi kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)

Tambaya: Idan muka zo daga garinmu muka yi Umara, bayan mun huta sai muke so mu sake yin wata Umarar alhalin muna cikin Makka, shin…

Tambaya: Idan muka zo daga garinmu muka yi Umara, bayan mun huta sai muke so mu sake yin wata Umarar alhalin muna cikin Makka, shin a gidajammu na Makka za mu yi Harama ko a Tan’im ko kuwa a wajen Mikatimmu na asali?
Amsa: Maimaita Umara a lokaci guda bai halatta ba, sai dai ku yawaita dawafi da Sallah da addu’a, a maimakon maimaita Umara, mutukar ka zo daga garinku ka yi Umara daya ta Ramadana ta isar maka.
Amma idan ka zo ka yi Umara ba ta Ramadana ba, sai ka so ka zauna ka samu ta Ramadana, babu laifi kan hakan, sai dai ba za ka yi Harama daga gidanka ba, sai ka yi Harama daga Tan’im ko Ja’aranata, ko daga Arafa, wato ka fita bayan gari ka sami tafiyar wasu ’yan milamilai, amma wajen da ya fi maka kusa shi ne Tan’im, ka yi Haramarka daga can ka zo ka yi Umara. Wannan muna magana ne idan dama ba ka zo don yin Umara Ramadana ba ce. A fahimta idan ta Ramadana ce ba za a sake yin wata ba, domin Sahabbai ba sa maimaita Umara sai dai su yi ta dawafi suna Sallah suna addu’o’i da karanta Alkur’ani.
Tambaya: Shin wanda ba a kewayen kasar Makka yake ba, zai zo a jirgi ya halatta ya yi Harama a cikin jirgin idan an zo daidai inda Mikati yake?
Amsa: kwarai ya halatta idan ya zo daidai inda Mikati ya ke a yi Harama, sai dai dole ne, sai ya yi wanka tun a garinsu idan ya zo saitin Mikatin sai ya yi niyya ya kama fadin Labbaika, amma kamata ya yi ya tube kayansa ya sanya Hirami, da ya zo saitin wajen sai ya yi niyya, hakan ma shi ne ya fi, domin idan ya ce sai ya zo wajen zai yi komai, to kafin ya farga jirgi ya yi tafiya mai nisan da ya wuce wajen Mikatin.
Tambaya: To, idan kuma mutum ya yi niyya kafin a zo wajen Mikati fa?
Amsa:  Hakan ya halatta sai dai ba a so, amma in ya yi niyyar ce don tsoron kada a wuce bai sani ba wannan babu komai.
Tambaya: Idan mutum ya taho ta Gabas zai zo Makka don Umara a ina zai dau Harama?
Amsa: Zai dauki Harama ne idan ya zo saitin Mikati, idan kuma a jirgi yake sai ya yi wanka a kasarsu ko a Riyad ko ma dai a ina ne, abin nufi shi ne : a yi wanka a tsabtace jiki a sanya turare Sunnah ne, idan ka hau jirgi in an kusanci Mikati sai ka sanya harami, da an zo inda Mikati yake sai ka yi niyya ka fara Talbiyya (fadin Labbaika…..), idan ma ka yi niyyar kafin a karaso Mikati don gudun kada a wuce saboda saurin jirgi wannan babu komai. Sayyidina Umar (RA) yakan ce da wadanda ba su wuce ta wajen Mikati ba, cewa: “Ku duba ku kardadanci inda yake a kan hanyarku.” Buhari ne ya rawaito.
Tambaya: Mun yi niyyar yin Umara daga gida inda ba kasar Sa’udiyya ba, da muka zo filin jirgin Zaharan sai muka yi Harama, daya daga cikinmu kuwa tun a jirgi ya yi Harama, wasu kuma sai da aka sauka a filin jirgi, amma ba mu yi raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba, mene ne matsayin hakan?
Amsa: Babu laifi domin raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba tilas ba ne, idan ka yi su, ya fi kyau, in kuwa ba ka yi ba, ba ka da wani laifi, haramarka ta yi, kuma da wanda ya yi Harama tun a cikin jirgi da wanda sai da a ka zo filin jirgi ya yi duk haramarsu ta yi, muna fata Allah Ya karba.
Tambaya: Ni dalibi ne dan shekara 21, yau kwanana uku da zuwa daga Amurka, na yi yawo a jirgi daga nan zuwa can har na iso Jiddah ba ni da Harami, da yamma na tafi Makka a gajiye da gari ya waye sai na tafi da’ifa don in dauki Harama a can mene ne hukuncin hakan ?
Amsa: Babu laifi abin da ka aikata ka yi daidai, matukar cewa ka zo ne don yin Umara to ka tafi inda Mikatinka yake shi ne abin da shari’a ta ce, amma da a ce zuwan da ka yi ba ka zo ne don yin Umara tun asali ba, sai bayan da ka isa Makka sannan ka yi niyyar yin Umara da sai ka yi Haramarka a Tan’im, Umararka ta yi muna fatan Allah Ya karba.
Tambaya: Mutanen gida daya ne suka sauka a Mina amma ba su yi Harama ba, mutum biyu a cikinsu suka tafi Makka don samar musu masauki, daga baya suka dawo Mina suka je gidan wanka suka yi wanka suka yi Harama, ya ya hukuncin wadancan mutum biyun yake inda suka shiga Makka ba su yi
Harama ba, sannan suka dawo Mina suka yi Harama a can?
Amsa: Wato ke nan sun koma wajen da ya kamata a ce daga can suka yiwo Harama, babu komai kan hakan kuma hakan ma da suka yi shi ne abin da ya fi dacewa
Tambaya: Mace ce ta zo Makka ta wuce Mikati ba tare da niyyar shiga Harama ba, saboda ba ta da isasshiyar lafiya, yanzu kuma tana Makka, a ina ya kamata ta yi Harama don yin Umara?
Amsa: Matukar cewa ba ta shigo da niyyar Umara ba, wata larurar ce ta kawo ta, to babu komai a kanta, idan kuma daga baya tayi niyyar yin Umara, sai ta yi haramarta a Tan’im, amma idan tun farko Umara ce ta kawo ta, to a baya mun fadi cewa dole sai ta dawo inda Mikati yake ta yi Harama, idan kuwa ta yi Harama daga Makka to sai ta yi yanka.
Tambaya: Mene ne hukuncin wuce Mikati ba tare da Harama ba?
Amsa: Hakan ya halatta, matukar cewa ba ka zo ne da niyyar yanka ba, ya halatta ka shiga Makka ba tare da Harama ba, idan ka zo ne ba da niyyar Umara ko Hajji ba, kawai dai ka zo ne don wani dalili naka kamar neman ilimi, ko duba mara lafiya, ko kasuwanci, kai ko ma a ce hanya ce ta biyo da kai, wannan babu komai a kanka. Wanda dole sai ya shiga da Harama shi ne wanda ya zo don aikin Hajji ko Umara, idan ya wuce ba tare da ya yi Harama ba, to sai ya zub da jinni, ma’ana sai ya yi yanka.
Tambaya: Ni mutumin kasar Saudiyya ne ina aiki a kasashan waje, a watan azumi na zo, iyalaina suna Jiddah, na fara sauka a wajensu na yi kwana uku, sannan daga baya na yi Haramar yin Umara, shin ina da laifi?
Amsa: Wannan zuwan da kai ka zo ne don iyalanka, sai bayan ka je gida sannan ka yi niyyar yin Umara, yin haka babu laifi, sai ka yi Harama a Jiddah kamar yadda ’yan cikin Jiddah za su yi.