Na Abdullahi bin Muhammad bin Abdul’Aziz bin Humaid
Fassarar Imam Ahmad Adam Kutubi
Tambaya: Wani mai tambaya na cewa: yana da mahaifiya tana so ta yi Hajji sai dai ta yi nisa da yawa, ita kuma ba za ta iya hawa mota ba, shin ya halatta ya yi mata Hajji?
Amsa: Idan ba za ta iya hawa jirgi ko mota ba, babu laifi ka yi mata Hajji in ta yarda, amma idan za ta iya zuwa, to, dole nesai ta yi Hajjin Farilla da kanta, bai halatta a yi mata Hajjin Farilla ba matukar za ta iya yi, sai dai in ba za ta iya ba.
Tambaya: Ni mutumin Siriya ne na yi Hajji sau biyu, mahaifiyata ma ta yi, dan uwana kuma ya yi wa mahaifimmu. Ina da ’ya’ya bakwai duk yara, matata kuma tana gida ba za ta iya barin yara su kadai a gida ba, shin zan iya yi mata Hajji?
Amsa: Idan tana da karfin da za ta iya, kuma Hajjin Farilla ne, to dole ta yi da kanta, amma idan na nafila ne, to babu laifi in ta yi Izini. Ba a yi wa mutum Hajjin Farilla matukar yana da karfi da iko kuma zai iya yi, idan yara sun girma dole ta je ta yi ko kuma a nemo wacce za ta zauna a gidan ta kula da yara.
Tambaya: Idan na yi niyyar wakiltar wani a Hajji, ni kuma a niyyata so nake na yi Hajji da Umara, shin dole ne sai mun yi da shi cewa Hajji da Umara, ko kuwa in na ce masa Hajji kawai ya isa?
Amsa: Idan ka wakilta wani kan Hajji ya kamata ka fada masa cewa Hajji da Umara kake so, idan ba ka fada masa ba Hajji ne kawai a kansa, saboda Umara aiki ne mai zaman kansa da niyyarta, Hajji ma haka, shi iyaka abin da kuka yi da shi kawai zai yi maka.
Tambaya: Idan aka wakilta mutum ya yi wa wani Hajji aka biya shi, shin Allah zai ba wanda aka wakilta din lada?
Amsa:Bai kamata ka karbi lada don za ka yi wa wani Hajji ba, sai dai idan kai mabukaci ne, ba kamar yadda mafi yawan mutane suke yi suna mai da ita kamar hanyar neman kudi ba, hakan bai kamata ba. Abin da ya dace shi ne ya zamto kai manufarka ita ce kana son zuwa Makka amma ba ka da dama, to a nan idan ka samu wanda zai biya ka, ka yi masa babu laifi ka karbi abin da zai ishe ka ka je Makka ka yi dawafi, idan ka yi masa Hajjinsa ragowar lokutan naka ne sai ka yi sallolinka na farilla da na nafila, ladan naka ne, ka yi dawafin nafila ladan naka ne ka yi addu’o’i, abin da kawai yake na wanda ya biya ka shi ne dawafin ifada da Safa da Marwa da Tsayuwar Arfa da Jifa da Kwanan Mina, amma duk sauran ayyukan da ba sa cikin ayyukan Hajji, to ladansu naka ne.
Tambaya: Zan yi wa wani Hajji, ya ba ni Riyal dubu biyar, abin da aka kashe kuma Riyal dubu uku, shin ya halatta na rike sauran?
Amsa: Shari’a ta yarda ka karbi wani abu a wajen wanda za ka yi wa Hajji, idan ba ka da kudi, amma ba wai ka karbi kudin don kamayar da harkar sana’a ba. A’a abin da ake so ya zama kai ma kana da shaukin
zuwa Makka ka yi ibada, sai ka yi amfani da wannan dama amma ba wai ka mayar da harkar wani fagen samun kudi ba. Amma idan ka karbi Riyal dubu biyar, ka kashe dubu uku idan wanda ya ba ka ya yarda shi ke nan, tunda idan ka karbi kudin amma ba ka yi Hajjin ba, sai ka biya shi kudinsa, ko kuma ya ba ka dubu biyu sai ba su ishe ka ba, sai da ka kashe dubu uku kana da ikon zuwa wajensa ya cika maka kudinka, idan kuma wani abu ya yi ragowa sai ka dawo masa da shi in ya yarda ya bar maka shi ke nan, wannan shi ne abin da malamai suka tabbatar.
Tambaya: Ni ina aiki ne a wata ma’aikata amma mai gidammu ya ki ya ba ni dama in je in yi aikin Hajji, sai muka hada ba ki da abokan aikina kan su kular min da aikina in je in yi Hajji in dawo shin hakan ya
halatta?
Amsa: Hajjinka ya yi, sai dai albashin da kake karba a kwanakin da ba ka aiki ka ci haramun, kana da ’yanci ka tafi ka yi aikin Hajji amma kada ka karbi albashi idan ba ka yi aiki ba, don haka sai ka mayar musu da albashin da ka karba ba ka yi aiki ba.
Tambaya: Ina ne wajen da bakar fata za su dauki Harama game da Alhajin da zai fara zuwa Jiddah?
Amsa: Wajen daukar Haramar kasashen bakar fata musamman wadanda za su biyo ta wajen Jiddah, Malaman Mazahabar Hambaliyya sun ce sai su dauki Harama a garin Jidda, saboda ba su biyo ta inda mikatinsu yake ba. Amma Babban Malamin nan Hafiz Ibnu Hajar Al-Askalani a littafinsa Fatahul Bari cewa ya yi: “Za su yi Harama ne idan sun zo daidai inda asalin mikatinsu yake, saboda dole ne mutum sai ya biyo ta wajen mikati koda bai gan shi ba. Saboda Annabi (SAW) ya sanya wa mutenan Madina mikatinsu ya zama Zu-Khulaifa, mutanen Yaman kuma Yalamlama, mutanen Najad kuma karnul Manazil, mutanan Gabas kuma Juhufa. To ta duk inda mutum zai zo aikin Hajji ko daga ina yake a duniya dole sai ya biyo ta daya daga wadannan wurare ko daura da su, to idan ya zo kwatankwacin inda suke sai kawai ya yi Harama a wajen. Wasu malaman kuma suka ce: Mutum ya yi Harama a garin Jiddah, musamman wadanda suka taho ta wajen Sudan saboda hanyarsu ta saba wa Yalamlama ta kuma saba wa Juhufa.”
Tambaya: Mene ne hukuncin mutumin Makka da yake so ya yi Umara, zai yi Harama daga gidansa ne ko kuwa sai ya je Tan’im ko Ja’aran zai daura Harami?
Amsa: Bai halatta ya yi Harama daga gida ba, idan ya yi haka sai ya yi yanka (fidiya), sai dai ya yi Harama daga Hillu, domin ko a bangaren ina gidansa yake abin da ake so shi ne ya fita wajen gari ya yiwo Harama daga can.
Tambaya: Mu mutanen Makka ne, mun saba kowane watan Ramadan muna yin Umara amma daga gidajenmu muke daukar Harama, sai kuma mu tafi Tan’im mu dauki niyya, shin hakan da mu ka yi ya yi ko kuwa dole sai a Tan’im za mu daura Harami?
Amsa: Abin da kuka yi ya yi babu laifi, matukar cewa ba ku yi niyyar Umara ba sai a Hallu, to hakan ya halatta, insha Allah babu laifi.
Tambaya: Matata ta zo daga Gabas da dadewa ba ta yi Umara ba, sai a yanzu take so ta yi Umara, shin sai na mayar da ita inda mikatinsu yake ta yi Harama, ko kuwa ta yi Haramarta a Makka tunda a nan muke a zaune?
Amsa: Idan lokacin da ta shigo ba ta shigo ne da niyyar yin Umara ba, saboda a nan kuke zaune, to, idan za ta yi Umara ba sai ta koma wajen mikatinsu na asali ba, sai kawai ta yi Harama daga Tan’im, tunda daga baya ta yi niyyar Umarar, sai kawai ta yi a Tan’im wajen da yanzu ake kira da Masallacin Nana A’isha.