✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zababben Mataimakin Gwamna ya jinjina wa Kamfanin WACL

Zababben Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, ya yaba wa Kamfanin WACL da RESL kan kafa sabon wurin baje kolin kayayyaki a birnin…

Zababben Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, ya yaba wa Kamfanin WACL da RESL kan kafa sabon wurin baje kolin kayayyaki a birnin Maiduguri.

Kamfanin na WACL, yana harkokin kayan gini irin su duwatsun kawata gida da kayayyakin zayyana gine-ginen siminti na zamani da sauransu.

Ya yi jinjinar ce, yayin bikin bude katafaren shagon kayayyakin da ya gudana a birnin Maiduguri, wanda shi ne na farko da aka bude a kan hanyar Damboa.

Zababben  Mataimakin Gwamnan, wanda Daraktan Tsare-Tsare a Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ta Jihar Borno, Mista Samuel Bumba ya wakilta, ya yaba wa kamfanin a kan zuba jarin da ya yi wanda shi ne na farko irinsa a birnin Maiduguri, duk da irin kalubalen rashin tsaro da jihar ta fuskanta cikin shekara 10 da suka wuce.

Ya yi alkawarin bayar da goyon bayan gwamnatin jihar, wajen bunkasa jarin da kamfanin ya zuba, da zai samar wa dimbin matasa aikin yi, tare da dawo da harkar zuba jari a jihar.

A cewarsa, “Gwamnatin Jihar Borno, za ta tallafa wa kamfanin don ganin matasan Borno sun samu ayyuka a karkashin kamfanin da zimmar rage matsalar rashin aiki  ga matasanmu.”

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Borno, Alhaji Ahmed Ashemi da Shugaban Cibiyar Kasuwanci da Ma’adinai da Masana’antu da kuma Harkar Noma ta Jihar Borno, Farfesa Ibrahim Goni, sai Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi na Sashen Koyar da Ilimin Ma’adinai na Jami’ar Maiduguri da kuma Shehun Borno.

Da yake mayar da jawabi, Manajan Gudanarwar Kamfanin WACL, Alhaji Abdulrahim Bello, wanda ya yi jawabi a madadin Babban Manajan Kamfanin, Mista Bhaskar Rao ya ce wurin bajen kolin da aka bude hadaka ne a tsakanin kamfaninsu da Kamfanin Amood Projects, wanda babban kamfani ne a jihar ta Borno.

Daraktan ya ci gaba da cewa hadakar da kamfanin ya yi da Kamfanin Amood Projects an yi nazari sosai a kan hakan, wanda ke da zimmar ba da gudunmawa ta fuskar samar da gidaje masu rahusa kuma nagartattu da za su gogayya da irin wanda ake shigowa da su Najeriya daga kasashen Nahiyar Asiya da Turai, kuma ya yi daidai da nauyin aljihun ’yan Najeriya.

Shi ma Manajan Daraktan Kamfanin Amood Projects, Alhaji Sani Ibn Is’hak ya bayyana cewa wurin baje kolin hajojin shi ne irinsa na farko a birnin Maiduguri, kuma abin a yi maraba da shi ne.