Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta ce za ta ɗau mataki kan dakataccen kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Hudu Ari.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na INEC Festus Okoye ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels.
Hudu Ari dai ya jawo hatsaniya lokacin da ya bayyana Sanata Aishatu Ɗahiru Binani a matsayin wacce ta yi nasara a zaɓen da ba a kammala ba.
Zaben Adamawa: An ba da belin Kwamishina Hudu
An kama dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa
Hakan ta sa shugaban ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari ya bada umarnin a binciki duk kan jami’an tsaron da ke da hannu cikin lamarin.
Mr Okoye ya ce “Ƴan sanda sun gama bincikensu kuma nan da makonni kaɗan za a sanar da ƴan Najeriya abinda aka gano.
“A bisa doka, INEC ce za ta shigar da ƙararsa don haka za mu ɗau mataki da zarar ƴan sanda sun miƙa mana sakamakon binciken.”