✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi wa marayu suturar da ba ta tsufa – Shugaban Kwmaitin Marayu

Aminiya:  Za mu so ka gabatar da kanka? Umar Atana: Suna na Umar Lawal Atana nine shugaban kwamitin tallafa wa marayu na Jihar Legas  a…

Aminiya:  Za mu so ka gabatar da kanka?

Umar Atana: Suna na Umar Lawal Atana nine shugaban kwamitin tallafa wa marayu na Jihar Legas  a karkashin  kungiyar Jama’atul izalatil bidi’a wa’ikamatus sunnah. Da farko na jagoranci kwamitin marayun a matakin karamar Hukumar Agege sai Allah ya sanya wa abin albarka duba da irin gagarumar nasara da muka yi na nema wa marayun agaji, tare da bai wa marayu 673 abin da ya kama daga hula da riga da wando da takalmi ga maza, sai riga da zani da hijabi da takalma ga mata. Kaya a dinke muke ba su don mukan tantance marayun ne sannan mu gayyato teloli su auna su, a  wancan  lokacin wato shekarar 2016 cikin mako guda na karbi aikin, wato sallah karama  ta rage kwana bakwai a hakan muka yi aiki ganin yadda muka gabatar da aikin cikin nasara da tsari ne magabatan mu suka ba ni jagorancin kwamitin marayun a matakin jiha.

Aminiya: Wacce hanya kuke bin wajen tantance marayun da kuke bai wa tallafin?

Umar Atana: Akwai fom din da muka tanada wanda muke tantance bayanan marayun, muna bude masu fayil ne inda muke adana bayanan su, muna binkawa ko  suna zuwa makarantar addini ko ta boko, wadanda basa zuwa makaranta muna taimaka masu ta wanna fannin, to a wannan shekarar marayun da muka tallafawa sun karu kwarai, domin sun nunka har sau uku,  kasancewar aikin ya tashi daga matsayin karamar Hukuma zuwa jihar inda aka kawo min marayu daga sassa daban-daban na Jihar Legas, wadanda suka hadar da Ikeja da da Apapa da Mil 12 da Alaba da dai sauran wuraren da muke da al’ummar mu a Legas haka zalika tallafin bai tsaya ga yaran Mmusulmi kawai ba, domin a wannan shekarar akwai wasu yara biyu da suka zo mana duk da ba Musulmi ba ne mun tantance su mun kuma ba su tallafi.

Aminiya:  Wacce hanya kuke bi wajen nema wa marayun tallafi? 

Umar Atana: A wannan shekarar da na yi la’akari da yawan marayun sai muka kiyasta a kalla za su ci Naira miliyan 10 na yi musu tufafinsu da takalmansu da hijaban su da huluna, maza a yi musu aski mata, kuma a ba su kudin kitso sannan ranar sallah a gayyato su a ba su abincin sallah a ɗaibe masu kewa, sai na yi nazari yadda za a yi mu nemo taimakon naira miliyan 10, nan  na fito da wani tsari na boca, bocan  na yita ta naira miliyan daidai na kaita wajen mutum 10, a tsarin da na fitar ko da mutum daya ne ya saye su to bukata ta biya sai mu koma mu cigaba da aiki, in an samu rauni, kuma sai mu mayar da ita Naira dubu 500 in an samu mutum 20 bukata ta biya daga nan har Naira dubu 100 idan an gaza samun mutum 20 da za su biya to a haka muka shirya aikin, kuma alhamdulilahi ba mu samu mutum daya da ya yanki ta miliyan daya ba, amma mun samu mutum biyu da suka yanki ta dubu 500-500, sannan mutum guda ya yanki na dubu 250, kuma mutane da dama sun yanki ta naira dubu 100-100. Daga nan muka sassauto har zuwa dubu 50 muka kuma bai wa masu karamin karfi damar shiga cikin ladar, inda mukan je kasuwanni da masallatai, kuma alhamdulillahi jama’a sun tallafa kwarai da gaske ba abin da za mu ce sai sam barka, ’yan uwa da abokan arziki da sauran jama’a sun ba da gudunmawa yadda ya kamata.  Abin lura a nan shi ne wannan agaji bai takaita ga kungiyar Izala kawai ba, domin wanda ya fara yankan katin na Naira dubu 500 dan darika ne, kuma tallafin da ake bai wa marayu ba a nuna wariya ko bangaranci. 

Aminiya: Agajin da kuke bai wa marayun ya takaita ne ga kayan sallah? 

Umar Atana:  Tallafin da muke bai wa marayun bai takaita a sutura ko abincin sallah kawai ba, domin a yanzu muna shirin yi masu suturar da ba ta tsufa, wato ba su ilimi da tarbiya, tare da koya musu sana’ar dogaro da kai. A nan Legas muna da marayu a kalla dubu uku, sau tari yaran da kan zo a tattance su da yawan su za ka same su cikin bukata ta musanmman, za ka ga suna bukatar a kula da lafiyarsu, to wanda ke cikin irin wannan hali ai ko ka ba shi kayan sallah ba shi da wani mahinmmanci a gare shi. Don haka mukan kai su asibiti a kula da lafiyarsu kafin mu ba su kayan sallah. Shirin da muke yi na ba su Ilimi da tarbiya da koya musu sana’ar dogaro da kai ne ya sanya nan ba da jimawa ba za mu kafa musu gidauniya, inda za mu nema musu taimako, muna sa ran tara masu kuɗi naira miliyan 250 wanda in an samar masu wannan tallafi za mu bude musu cibiyoyin koyar da ilimi da tarbiya da koya musu sana’a, sannan za a dinga juya wannan tallafin ne, ta yadda ba sai duk shekara an fita ana yawo da kokon bara ba.