Birtaniya za ta ba wa Ukraine tallafin jiragen ruwa maras matuka da ka iya lalubo muggan nakiyoyin da Rasha ta binne a gabar teku, in ji ma’aikatar tsaron kasar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da da Sakataren Tsaron Birtaniya, Ben Wallace ya fitar a ranar Asabar.
- Ibrahim Ahmad: Makahon da ke saka kayan adon daki
- ’Yan sanda sun kama amarya kan laifin sata a wajen bikinta
Sanarwar ta ce jiragen na iya nutso mai cin dogon zango har mita 100 a kasa, kana kuma ana iya amfani da su a wuraren da ke sa sassaucin zurfi na ruwan teku a cikin hanzari.
Ko baya ga kyautar jiragen guda shida, DW ya kuma ruwaito Ma’aikatar Tsaron ta Birtaniya tana shan alwashin horar da jami’an sojin Ukraine yadda za su yi amfani da sabbin makamai a wani mataki na kare kansu daga mamayar Rasha.
Ana dai zargin ko akwai yiwuwar Rasha ta binne manyan nakiyoyi a karkashin tekun Ukraine don haddasa tarnaki wa gabar ruwa Bahar Aswad da Ukraine ke amfani da ita wajen fitar da kayayyakin abinci da take nomawa zuwa kasuwannin duniya.