✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu tabbatar an bi wa Ummita hakkinta —Ganduje

Zubar da jini ne, don haka dole maganar shari’ah ta shigo.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ce zai tabbatar da ganin shari’a ta yi aikinta a batun kashe Ummukulthum Sani Buhari, matashiyar da ake zargin wani dan China da aikatawa.

Gwamnan yayin wani jawabi a Fadar Gwamnatin Jihar ya ce, “Zubar da jini ne, don haka dole maganar shari’ah ta shigo” kuma sai doka ta yi aikinta.

Ya ce tuni suka sa aka kama mutumin da ake zargi, Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar ranar Juma’a.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai har cikin dakin matashiyar wadda aka fi sani da Ummita a gidansu da ke unguwar Jambulo ta Karamar Hukumar Gwale.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta mayar da batun zuwa Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka Bangaren Kisan Kai na Shalkwatar ’yan sanda da ke Bompai.

Yadda aka kashe matashiyar

Mahaifiyar Ummita, matashiyar nan da saurayinta dan kasar China ya yi wa kisan gilla a Kano, ta ce a gabanta abin ya faru.

A bayaninta bayan jana’izar ’yar tata mai shekara 23, mahaifiyar ta ce, dan Chinan ya ritsa ’yar ne a daki ya rika daba mata wuka.

Ta ce, “’Ya ta ce, yana yawan zuwa wurinta, amma tana kin kula shi.

“Da ya zo wannan karon sai ya yi ta kwankwasa kofa, da na ji yadda yake dukan kofar da karfi ya ishe ni sai na je na bude.

“Ina budewa sai ya ture ni gefe ya shiga cikin gidan ya fara caccaka mata wuka.

“Shi ne na yi ta kururuwa mutane suka shigo a guje, muka garzaya da ita zuwa asibiti, amma kafin mu isa rai ya yi halinsa.

“Abin ya faru ne da misalin karfe 9.30 na dare,” ranar Juma’a.

“Ni da ita da kannenta mata biyu ne a gidan a lokacin; dan uwanta ba ya nan, mahaifinta kuma ya rasu.

“A lokacin ana ruwan sama, mutane sun shige gidajensu, ba za su iya jin ihuna ba, sai da wani ya zo ya shigo ta taga.

”Ina rokon da dauki mataki kan wannan abin da aka yi wa ’yata.

Tsohuwar budurwarsa ce

Ta ci gaba da cewa marigayiyar, “Sun taba yin soyayya, amma ta yi aure, daga baya auren ya mutu.

“Bayan rabuwar aurenta ne ya sake dawowa, ya matsa cewa yana son ganin ta.

“Yakan shigo, duk da cewa ba ma son hakan, amma shi bai fahimta ba; Wani lokaci har korar sa muke yi.

“Da na ce zan yi karar sa wurin ’yan sanda sai ’ya’yana suka hana, suka ce ba sai an fitar da abin da ke faruwa duniya ta sani ba.”

Yadda aka kawo dauki

Ta ce, “Mutumin da ya kawo mata dauki ta taga ya shigo gidan, kuma shi ne ya kama shi ya fito da shi waje.

“Har ya tsere, amma suka bi shi suka kamo shi suka dawo da shi yanzu yana hannun ’yan sanda.

“Ita ce babbar ’yata mace, amma akwai maza biyu kafin ita.

Abin da ya sa ya kashe ta

“Ya fahimci ba ta son shi, idan ya kira waya ba ta amsawa, shi ya sa ya yanke shawarar harin da ya kawo.

“Ya kusa awa daya yana buga kofar, ita ce ta nemi in je in sallame shi, amma da na bude kofar shiga gidan ya ture ni ya shigo gidan.

“Kai-tsaye ya wuce zuwa dakinta, domin ya san dakinta, saboda yakan shigo gidan; yawanci ’yan uwanta maza ke tisa keyarsa daga gidan.

“A Shoprite suka fara haduwa lokacin da ta je sayen turare inda suka karbi lambar juna, daga baya suka fara waya.

“Da ta yi aure sai suka rabu. Har mijinta na zargin cewa suna chatting da shi; amma ba wannan ne sandaniyyar rabuwar auren ba.

“Tabbas ta fada mishi cewa za ta aure shi, amma da ’yan uwan mahaifinta maza suka ga wasu matsaloli sai suka ki amincewa, kuma na goyi bayan dalilansu,” in ji ta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce sai daga baya zai fitar da karin bayanai.