✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za mu nemi diyyar rayukan ’yan Arewa idan aka saki Nnamdi Kanu’

Matasan sun ce dole ne gwamnati ta biya diyyar wadanda aka kashe matukar aka saki Kanu.

Kungiyar Matasan Arewa (AYCF), za ta nemi diyyar rayukan ‘yan Arewa da aka kashe tare da lalata dukiyoyinsu a yankin Kudu maso Gabas muddin aka saki jagoran ‘yan awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

AYCF ta yi gargadin ne ta bakin shugabanta, Yerima Shettima wand ya ce sakin Kanu zai nuna rauni daga bangaren gwamnati.

Da yake tattaunawa da manema labarai, Shettima ya ce sakin shugaban na IPOB za a iya fassara shi da cewa gwamnati na tsoronsa kuma jami’an tsaro ba su da katabus.

Ya jaddada cewa kamata ya yi a yi amfani da shari’ar Kanu a matsayin wata aya don guje wa laifukan da za su faru a nan gaba.

A cewar Shettima: “Sakin Nnamdi Kanu saboda Gwamnatin Najeriya na tsoronsa? A sake shi saboda jami’an tsaron Najeriya na tsoronsa, wadannan mutanen kullum kashe ’yan Arewa da ke cirani a yankinsu.

“Dole ne doka ta dauki matakin da ya dace yayin da suka aikata ta’addanci kan ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da mutanensu.

“ Idan ba a samu komai a kan Kanu ba, a sake shi. Mu ba matsorata ba ne, kuma ’yan Najeriya ba za su iya zama matsorata saboda wasu mutane ’yan tsiraru ba.

“Idan gwamnati ko kotu suka yanke cewar za su sake shi, to su sani cewa za mu bukaci a biya diyya ga rayukan ‘yan Arewa da wadannan miyagun suka kashe.

“Mun riga mun samu bayanai na alkaluman‘yan Arewa da aka kashe da wadanda aka lalata wa dukiyoyi saboda za mu bukaci gwamnati ta biya mu diyya ga mutanen da muka yi asara, biliyoyin dukiyoyin da aka yi asara; dole ne gwamnati ta kasance cikin shiri don ta biya.

“Kawai gwamnati ta sani cewa lallai za mu fito neman diyya; tun da muna zaune a inda babu doka da oda.

“Za mu yi amfani da wannan shari’a ta Nnamdi Kanu a ko da yaushe a matsayin abin nuni ga duk wani laifi da za a aikata a nan gaba; kamata ya yi gwamnati ta kasance a shirye.”