✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu nemi Buhari ya zarce-Umar Shu’aibu

Shugaban Kungiyar Magoya Bayan Buhari, Alhaji Umar Shu’aibu ya ce za su dauki matakan da suka dace don jawo hankalin Shugaba Buhari ya sake tsayawa…

Shugaban Kungiyar Magoya Bayan Buhari, Alhaji Umar Shu’aibu ya ce za su dauki matakan da suka dace don jawo hankalin Shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
Shu’aibu ya yi furucin ne a tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya a Abuja a karshen makon da ya gabata.
Ya ce”Ba kowa ne ya san yadda ka’idojin Buhari suke ba. Ya fara tsayawa takara a shekarar 2003 bayan da aka nemi ya tsaya takara. Kowa ya san shi ya ci zaben shekarar 2003 da 2007 da kuma 2011 amma sai aka yi masa magudi.
“Bayan zaben shekarar 2011 ya ce ba zai sake tsayawa takara ba amma mu da muka san shi sosai mun san cewa idan ya ce ba zai sake tsayawa takara ba to za mu shiga matsala saboda ba mu da kamar shi a Najeriya. Saboda haka sai muka lallashe shi ya sauya ra’ayinsa ya sake tsayawa takara, sai muka tura masa tawaga inda daga bisani ya amince”. Inji shi.