✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kori duk malamin da ya nemi yin lalata da daliba –Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa

Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Farfesa Suleiman Mohammed ya ce a shirye mahukuntan jami’ar suke su hukunta duk wani malamin da ya…

Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Farfesa Suleiman Mohammed ya ce a shirye mahukuntan jami’ar suke su hukunta duk wani malamin da ya yi ko ya nemi yin lalata da dalibarsa.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen wani taron fadakarwa wanda wata cibiyar wayar da kan dalibai a kan al’amura da suka shafi jinsi a Babban Dakin taro na jami’ar a karshen makon da ya gabata. Shugaban ya bayyana cewa tuni mahukuntar jami’ar suka kafa wani kwamiti na musamman da zai rika yin sintiri yana kuma gudanar da bincike kuma a cewarsa duk wanda aka samu da laifin zai yaba wa aya zakinta musamman ta hanyar sallamarsa baki daya. Ya ce, “Ina so in kuma yi amfani da damar nan in gargadi malamanmu a jami’ar nan cewa hukuncin duk wani malami da aka samu ya aikata irin wannan laifi kora ce tare da tabbatar da an dauki duk matakai da suka dace akansa don ya kasance darasi ga saura masu niyar yin haka.” Daganan ya jinjina wa cibiyar da ta shirya taron dangane da kokari da take yi wajen fadarkar da daliban da malamansu baki daya inda ya yi alkawari cewa jami’ar za ta tabbatar ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya don samun nasara kan abubuwa da cibiyar ke kokarin kawarwa a tsakanin daliban da malamansu baki daya, sannan ya shawarci mahalarta taron da su tabbatar sun yi amfani da abubuwa da aka koya musu a lokacin taron don kare mutuncin da jami’ar ke da ita tun bayan kafa ta.

A nata vangaren, Daraktar Cibiyar Hajiya Hauwa’u Mainoma ta bayyana cewa wannan taron fadakarwa mai matukar muhimmanci shi ne karo na 2 da aka gudanar tun bayan kafa cibiyar a jami’ar a shekarar 2017, inda ta kara da cewa a sakamakon aukuwar laifuffuka da dama a jami’ar da sauran manyan makarantun jihar da kasa baki daya musamman wadanda suka shafi cin zarafin dan Adam musamman mata ta hanyar  yin fyade da lalata da su ne ya sa cibiyar ta ga ya dace ta shirya taron don wayar da kan daliban da malamansu baki daya musamman game da hanyoyin kare aukuwar lamarin da illolinsu da sauransu. Dana nan sai ta yi kira ga gwamnatoti a duka matakai da hukumomi da abin ya shafa a jihar da kasa baki daya da su tashi tsaye su tunkari lamarin domin yakarsa baki daya.

Taron ya samu halartar daliban jami’ar da dama musamman mata da malamansu da sauran manyan baki daga ciki da wajen jami’ar.