✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a zaftare Naira miliyan 830 daga albashin Luis Suarez idan ya kara cizo

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya gargadi sabon dan wasan gabansa Luis Suarez wanda ya sayo shi daga kulob din Liberpool na Ingila…

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya gargadi sabon dan wasan gabansa Luis Suarez wanda ya sayo shi daga kulob din Liberpool na Ingila cewa idan ya kuskura ya sake cizon wani dan kwallo a nan gaba kulob din zai zaftare masa albashin Fam miliyan uku kwatankwacin Naira miliyan 830 a matsayin hukunci.
Shi dai Suarez ya kasance shi ne dan kwallo mafi tsada da kulob din Barcelona ya taba sayowa a tarihin kulob din.  dan kwallon zai rika karbar albashin Fam dubu 200 kwatankwacin Naira miliyan 53 a duk mako. Tuni  dan kwallon ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyar.
Sai dai wasu rahotanni sun ce kulob din FC Barcelona sai da ya ajiye wa Liberpool zunzurutun Fam miliyan 75 kwatankwacin Naira biliyan 20 kafin ya sayi Suarez daga Liberpool amma kulob din ya ce a Yuro miliyan 80 ya saye shi.
Albashin Suarez a FC Barcelona ta sa yanzu shi ne na hudu a jerin ’yan kwallon da suka fi karbar albashi a kulob din.  Lionel Messi shi ne na farko sai Neymar sai Andre Iniesta sannan sai shi Suarez din.
Sannan  Suarez ya kulla yarjejeniya da kulob din cewa ya yarda a rage masa albashi a tsakanin kashi 15 zuwa 30 idan ya sake aikata ba daidai ba a tsawon shekarun da zai kwashe.