✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi wa yara 850,000 rigakafin cutar Kyanda a Kebbi

Za a yi wa yara 850,000 masu fama da cutar kyanda rigakafi a Jihar Kebbi. Gwamnatin Jihar ta hada hannu ne da hukomomin UNICEF, WHO,…

Za a yi wa yara 850,000 masu fama da cutar kyanda rigakafi a Jihar Kebbi. Gwamnatin Jihar ta hada hannu ne da hukomomin UNICEF, WHO, da NPHCDA, kuma an fara aiwatar da shirin rigakafin cutar ne na 2017/2018 a karamar hukumar Bagudo ta jihar a ranar Asabar da ta gabata.

Yankunan da za a yi rigakafin  a mataki na farko su ne Bagudo, Sakaba, Fakai, Zuru, Suru, Koko/Besse, Yauri, Dandi da sauransu. Mataki na biyu kuma zai hada da Birnin Kebbi, Aliero, Jega, Kalgo, Gwandu, Miyama da sauransu.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Kiwon lafiya ta jihar, Hajiya Halima Dikko ta ce a lokacin da take kadddamar shirin “aiwatar da irin wannan rigakafin ana yinshi ne a lokacin da ya fi dacewa, kuma muna sa ran a yi wa yara 850,000 rigakafin wannan mummunar cutar a Jjihar Kebbi.”