✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a kara albashin ma’aikata a Legas

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi yi wa ma'aikatan jihar karin albashi ya zama wajibi saboda yanayin tsadar rayuwar.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar karin albashi.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin raba sabbin motoci na alfarma guda 100 ga wasu daraktoci a ma’aikatun gwamnati.

Sanwo-Olu ya ce zuwa karshen wannan wata za a fara raba motoci ga wasu daraktocin jihar.

Ya yi albishir din ne yayin ziyarar da ya kai sakatariyar gwamnatin jihar a ranar Talata.

A cewarsa, yi wa ma’aikatan karin albashi ya zama wajibi duba da yanayin tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Sai dai bai bayyana yawan abin da za a kara a albashin ba, ko lokacin da za a fara biya, duk da cewa ya ce an kammala dukkan tsare-tsare.

Ya nuna godiyarsa ga ma’aikatan bisa hadin kai da goyon bayan da suka bai wa gwamnatinsa tun kafuwarta zuwa yau.