Jami’in Kula da Ayyukan Gwamnatin Tarayya a Jihar Legas, Olukayode Popoola, a ranar Lahadi ya ce za a rufe hannu daya na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan na tsawon kwana shida.
Ya ce za a dauki matakin ne don a samu damar kammala aikin a kan lokaci.
Olukayode, a cikin wata sanarwa ya ce matakin zai ba kamfanin gine-gine na Julius Berger, wanda ke gudanar da aiki a daya daga hannuwan, damar zuba kwalta daga Arepo zuwa Warewa, mai tsawon kilomita daya da rabi.
Jami’in ya kuma ce rufewar za ta shafi hannun da ke zuwa Legas ne kawai.
Ya yi kira ga masu amfani da hanyar da su ba da hadin kai, inda ya ce an tanadi jami’an tsaron da za su rika kula da ababen hawa don kaucewa cunkoso.
“Gwamnatin Tarayya ta himmatu matuka wajen kammala babbar hanyar Legas zuwa Ibadan kafin badi, saboda haka akwai bukatar a kara azama.
“Kamfanin Julius Berger zai zuba kwalta daga Arepo zuwa Warewa, kuma za a rufe hannu daya na kwana shida.
“Muna kira ga jama’a, musamman wadanda lamarin zai shafa da su yi mana uzuri,” inji shi. (NAN)