Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kara mafi karancin albashi a shekarar 2024.
Ngige ya kuma gargadi kungiyoyin kwadago da su daina tsoma kansu a harkokin gwamnati da kuma nada mukamai.
- Firimiyar Ingila na bincikar City kan badakalar kudade
- DAGA LARABA: Dalilin tallata kanmu a ‘Soshiyal Midiya’ don neman miji —’Yan Mata
Ya kuma ce ‘ya‘yan kungiyar na karya dokar da ta tilasta wa duk wani sabon dan kungiya samun horo na musamman a makarantar horon kwadago ta (MINILS).
Kazalika a taron Kungiyar Kwadago na Kasa karo na 13 da aka gudanar ranar Talata a Abuja, ya ja hankalin ‘yan kwadagon da su tabbatar da gwamntocin jihohi na aiwatar da Dokar Diyyar Ma’aikata ta 2010 (ECA) da doka ta ce a biya su.