✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Za a kafa hukumar kula da magunguna a Filato

Dokar ba karamin alfanu za ta kawo ga rayuwar al’ummar jihar ba.

Gwamnan Filatu Simon Lalong ya sanya hannu kan kudirin sabuwar dokar samar da Hukumar Kula da Magunguna a jihar.

Gwamnan ya sanya hannu kan kudirin dokar mai sashi 11, da kananan sassa 52 a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Jos, a ranar Alhamis.

Bayan sanya hannun ne kuma, ya ce dokar ba karamin alfanu za ta kawo ga rayuwar al’ummar jihar ba.

“In dai aka dabbaka dokar kamar yadda aka tsara ta, za ta saukaka wa al’umma samun magunguna masu inganci da rahusa a asibitocin jihar da na manyan makarantu, hadi da na duba gari,” in ji gwamnan.

Ya kuma gode wa ’yan Majalisar Dokokin jihar, bisa gaggawar mayar da hanakali kan kudirin, da kuma gaggauta zartar da dokar.