✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a iya amfani da baiwata wajen shirya kayataccen fim – Mai Kwaikwayon Murya

Zaharadden Abdussalam dan kimanin shekara 20 dan asalin karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna ne. A yanzu haka dalibi ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya…

Zaharadden Abdussalam dan kimanin shekara 20 dan asalin karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna ne. A yanzu haka dalibi ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Bichi kuma yake ajin farko. A tattaunawarsa da  Aminiya ya ce da masu shirya fina-finan Hausa za su yi amfani da baiwar da Allah Ya yi masa ta kwaikwayon murya da sarrafa jikinsa na yaro zuwa na tsufa da an samar da wani kayataccen fim da zai burge masu kallo. Kuma ya ce dabi’ar sanin wani a harkar shiga fim ita ce babbar kalubalen da yake fuskanta a halin yanzu:

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice? Sunana Zaharaddedn Abdussalam. An haife ni a garin Giwa ta Jihar Kaduna. Na yi karatun firamare da sakandare a can Giwa. A yanzu kuma ina ajin farko a FCE Bichi da ke Kano. 

An ce kana da baiwar kwaikwayon muryar mawaka ko za ka yi mana bayani?

Nakan iya kwaikwayon muryar mawakan Hausa, misali irin su danmaraya Jos da Aminu Alan Waka da Nazifi Asnanic da sauransu. Kuma nakan iya sarrafa jikina in koma tsoho ba tare da na sanya komai a fuskata na daga gemu ko wani abu makamncin haka ba. Kuma idan na tashi komawa tsohon ba wai kawai a kamannina abin yake tsayawa ba har da murya. Za ki ji muryata ta koma irin ta tsofaffi. 

Game da kwaikwayon muryar mawaka, ko hakan yana da nasaba da yawan sauraron wakokinsu da kake yi?

Gaskiya ba na jin hakan ne, domin idan hakan ne da wadansu sun yi, saboda akwai wadanda suka fi ni sauraron wakokin mawakan, amma ba su iya ba.  Za ki ga ko masu kwaikwayon waka idan suna sauraron waka wanda ake kira ‘mamming’ sai dai ki ga suna bin wakar ne amma muryarsu daban da ta masu ainihin wakar. Allah ne Ya ba ni wanann baiwar cikin sauki kawai. Abin da za ki gane shi ne ni fa ba wai kawai sai waka nake kwaikwayo murya ba. Idan har na taba jin muryarka ko muryarki, to zan iya kwaikwayon maganarka ko maganarki. 

Ba ka ganin wannan baiwa taka za ta fi yin amfani a harkar fina-finan Hausa maimakon kwaikwayon muryar kawai?

Kamar yadda kika fadi ni ma na yi wannan tunanin, hakan ya sa na je na samu wasu furodusoshin fim din Hausa guda biyu, amma sai dai hakata ba ta cimma ruwa ba. Saboda cikinsu babu wanda ya ba ni kwarin gwiwa a kan lamarin. Kin ga da farko dai na je wajen mawaki Ado Gwanja don ya hada ni da ’yan fim amma lamarin bai yiwu ba. Kuma wallahi ina matukar sha’awar yin fim, sai dai rashin samun goyon baya daga ’yan fim din da kuma rashin dama. Kin san yanzu harkar Najeriya wai sai ka san wani kafin a ba ka wani aiki. 

 Idan da za a ba ka dama a fim wacce irin rawa kake tunanin za ka iya takawa?

Ina ganin za a iya amfani da baiwata wajen samar da fim wanda ba a taba yin irinsa ba, domin za a iya nuna ni a matsayin tsoho da kuma yaro a lokaci guda. Kasancewar ba a taba samun irin wadanan fina-finai ba ina ganin za a iya samun wani sauyi ke nan. 

Wane kira kake da shi ga masu shirya fim din Hausa?

Ina kira gare su da su rika saurarar mutane a yayin da suka zo da wasu tunani ko tsari da suke tunanin za su kawo sauyi da ci gaba a masana’antar, domin idan sun duba ire-iren baiwarmu za ta taimaka musu wajen gudanar da sana’arsu. Ita baiwa da kike gani akwai dalilin da Allah Yake yin ta tare da bayar da ita ga duk wanda Ya so.