Za a fitar da gawar Fir’auna, Sarkin Masar da ya yi zamani da Annabi Musa (AS) da sarakunan Masar na shekaru aru-aru a wani gagarumin biki a ranar Asabar.
An shirya kayataccen bikin ne don dauke Fir’aunoni 22, maza 18 da mata hudu, zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi ta yadda masu yawon bude ido za su fi kayatuwa da ganin su.
’Yan bindiga sun kashe Shugabannin Fulani
An fara yi wa maniyyata aikin Hajji rigakafin COVID-19
Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
“Mun zabi mayar da su Gidan Tarihin Zamani ne saboda muna so, a karon farko, mu rika nuna su cikin wayewa da ilimi, sabanin yadda a baya suke a matsayin kayan wasa,” inji masanin kimiyyar tarihin kasar, Zahi Hawass.
Ya ce za a dauke su ne daga Gidan Tarihin da ke Dandalin Tahrir a birnin Alkahir zuwa Gidan Tarihin Kasar Masar da ke Fustat, babban birnin Masar a zamanin Daular Bani Umayyyah.
An kuma ware wa kowane Fir’auna mota ta musamman da za ta dauki akwatin gawarsa da ke lullube da sinadarin Nitrogen don tabbatar da cewa ba su samu wata illa ko barazana ba.
Jerin gwanon zai kasance ne bisa jerin zamanin mulkin sarakunan na kasar Masar, kuma cikin tsauraran matakan tsaro.
An rufe manyan hanyoyin yankin Kogin Nilu daga Dandalin Tahrir zuwa Fustat mai nisan kilomita biyar saboda ’yan kallo su samu damar kashe kwarkwatar idanunsu.
Sauya wa Fir’aunoni makwanci wani mataki ne na jan hankalin duniya zuwa ga abubuwan tarihin na musamman da suka kebanci Masar, bayan dokokin COVID-19 sun kawo koma-baya ga harkar yawon bude ido.
Masu binciken kimiyyar tarihi sun gano Fir’aunonin ne a wata tsohuwar makabartar sarakuna da tarihinta ya kai shekara 1871, a Deri Al Bahari da ke Luxour.
Mafi dadewa a cikinsu shi ne Seqenenre Tao, sarki na karshe a Daula ta 17, wanda ya rayu a karni na 16 kafin zamanin Annabi Isa (AS), kuma tarihi ya nuna ya yi mummunar karshe.
ِِAkwai kuma Ramses II, wanda wasu masana tarihi ke ganin shi ne ya yi zamani da Annabi Musa (AS); sai kuma Seti I, da Ahmose-Nefertari.
“Yin hakan cikin shagali da kawa shi ne abin da ya fi dacewa da gawarwakin; Su ne sarakunan Masar, Fir’auna. Wannan shi ne girmamawa a gare su,” inji Salima Ikram, wata mai binciken Kimiyyar Tarihi a Jami’ar Amurka da ke birnin Alkahira.